Posts

Showing posts from January, 2019

MAJALISAR DOKOKIN JIHAR NEJA TA GAYYACI SAKATAREN GWAMNATIN DA ALKALIN ALKALAN JIHAR

Image
Majalisar dokokin Jihar Neja ta gayyaci Sakataren Gwamnati Ibrahim Ladan tare da Alkalin Alkalai Nasara Dan-Malam  game da karin wa'adi da akayi wa shugaban Ma'aikata na Jihar. A ranar Laraba da ta gabata ne aka gayyace su domin suyi karin bayani game da karin wa'adin mulkin da akayi wa Shugaban Ma'aikar, Alhaji Yabagi Sule duk da cewa shekarun ritayar shi daga aiki ta cika. Shugaban ma'aikatan ya cika shekaru 60 ne a ranar 15 ga watan Janairu na wannan shekara wanda shine adadin shekarun ritaya daga aiki amma amma gwamnan ya kara mashi wa'adin mulki har zuwa 29 ga watan Mayu na wannan shekarar. Dan Majalisa mai wakiltar Agwarra a Majalisar dokokin Jihar ne wato Ahmed Bello ne ya gabatar da kudirin a gaban Majalisar. Dan Majalisar yace; Sashe na 208 sakin layi na (3) ya bada damar na Shugaban Ma'aikata dgaa cikin Sakataroran dindindin ko kuma wani mukami da yayi daidai da hakan. Hon Bello ya Kara da cewa " duk maiakata dole ne subi dokokin...

SANARWA DAGA RUNDINAR SOJOJIN NAJERIA

Image
Rundinar dakarun sojojin Najeriya ta bada sanarwar dakile wani hari da Kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram ta shirya kawowa a garin Baga na Jihar Borno. Mai magana da yawun rundinar ne wato Kanal Onyema Nwachuku ne ya sanar da haka a jiya Lahadi. Kanal Nwachuku ya Kara da cewa, Yan ta'addan sun so su kai mummunan hari wanda suke dauke da miyagun makamai tare da motoci biyu dauke da bindigogin harbo jirgin sama da kuma manya-mayan abubuwa masu fashe wa domin kai harin kunar bakin wake. An lalata mota daya dake dauke da kayan fashewa da kuma direban tare da 'yan ta'adda masu yawa. Haka kuma an kwato bindigogi da makamai masu yawa daga HANNUN 'yan ta'adda inda sojojij Najeriya suka bi su cikin daji.

SHARI'A TSAKANIN UWAR JAM'IYYAR APC DA HUKUMAR ZABE MAI ZAMAN KANTA (INEC): AN SA RANAR YANKE HUKUNCI

Image
Daga Aliyu B. Musa, Abuja. Babbar Kotun Tarayya da ke babban Birnin Tarayya Abuja ta sa ranar  22/1/2019 a matsayin ranar da zata yanke hukunci shari'ar da take yi wadda Uwar Jam'iyyar APC ta Kasa ta sa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa akan tilasta mata da ta amshi sunayen yan takarkarun ta na Jihar Zamfara. Idan baku manta ba Jam'iyyar APC a matakin Jihar Zamfara ta kasa gudanar da zaben fitar da gwani na Jihar har zuwa lokacin da aka rufe karbar sunayen yan takara a yayin da ita kuma uwar Jam'iyyar APC tace sun bada sunayen Yan takara ta hanyar yin sulhu. Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tace baza ta karbi sunayen  ba har sai Kotu ta bata izinin yin hakan. Haka kuma a ranar 22/01/2019 din ne ake sa ran Jam'iyyar zata bayyana sunayen 'Yan takarar da ta bada domin su daga tutar ta a zabe mai zuwa.

LABARI DA DUMI-DUMI

Image
Matasan Jukun sun  kona mota fiye da 25 a cikin tawagar Dan takarar Gwamnan jihar Taraba a karkashin Jamiyyar APC wato Alh Sani  Danladi Contact. An ji harbe-harben bindiga a lokacin da abun yake faruwa, amma dai har yanzu babu wani takamammen rahoto a kan rayuka da aka rasa.

KOTU TA BADA UMURNIN MAYARDA YAN MAJALISU 4 DA AKA DAKATAR

Image
Daga S. Sadiq, Gusau.. Babban Kotun dake Jihar Zamfara ta umurchi Majalisar dokokin Jihar karkashin jagorancin Rt. Hon Sanusi Garba Rikiji da ta mayar da Yan Majalisu 4 da ta dakatar ba bisa kan ka'ida ba. Yan Majalisun sun hada da: 1. Hon. Abdullahi Mohammed Dansadau 2. Hon. Malam Mani Malam Mumuni 3. Hon. Dayyabu Adamu Rijiya tare da 4. Hon. Mansur Ahmad Musa Bungudu. Alkalin Kotun ne Justice Bello Aliyu Dan-Daba ya bada umurnin ne yau a lokacin zaman Kotun a garin Gusau babban birnin Jihar Zamfara. Alkalin ya Kara da cewa wanna oda ta zama dole haka kuma ya zama dole a basu duk wani hakki na su a matsayin su na Yan Majalisu. Idan baku manta ba satin da ya gabata ne Majalisar dokokin Jihar Zamfara ta dakatar da wadannan Yan Majalisun ba bisa ka'ida ba inda suka kalubalanci wanna hukuncin a Kotu.

LABARI DA DUMI-DUMI: KOTU TA BADA UMURNIN MAYAR DA YAN MAJALISA 4

Image
Babbar Kotun Jihar Zamfara ta umurchi Majalisar dokokin Jihar Zamfara da ta mayar da Yan Majalisu 4 da ta dakatar ba bisa Ka'ida ba. Zamu kawo maku cikakken rahoto akan wanna labarin.

RIKICIN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA: GWAMNA YA GANA DA YAN MAJALISU MASU GOYON BAYAN SHI

Image
Daga S. Sadiq, Gusau. Gwamna Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara ya gana da 'Yan Majalisu su 17 masu goyon bayan sa ranar litinin 14/1/2019 a gidan gwamnati dake fadar gwamnatin Jihar dake garin Gusau hedikwatar Babban Birnin Jihar. A lokacin ganawar, Gwaman yayi alkawarin baiwa duk Dan Majalisar da bai samu tikitin komawa Majalisar dokokin Jihar ba wani mukami. Mukaman sun hada da Kwamishinoni, Mataimaka na Musamman wato S.A da kuma Chiyamoma na kananan hukumomi.  Da yake magana da yawun Yan Mjalisun su 17, Hon. Aminu Abubakar Danjibga ya jaddada goyon bayan su zuwa gare shi inda har yayi bayani na karyata taimakon da akace sunyi zuwa ga wata makarantar Islamiyya ta Aisha dake garin Bungudu. Hon Danjibga ya kara da isar da sakon Sanata Ahmad Sani Yarima na cewa kada Yan Majalisu masu goyon bayan gwamnati su yadda su hada kai da sauran 'Yan Majalisu masu goyon bayan Kungiyar nan ta G8 domin suna da kudurin tsige Kakakin Majalisar wanda zai basu dama har zuwa tsige...

ME YASA SHUGABA BUHARI KE NEMAWA ÝAN JAM'IYYARSA AGAJIN ƘURI'UN JAMA'A?

Image
Daga Mukhtar Jubril, Bauchi.     Na zo da wannan tambayar ne kuma zan amsata, bayan ganin yadda masu adawa suke neman ɗaukar hankalin jama'a tare da neman danƙarawa jama'a ƙin lafiyayyen shugaban nasu, don kawai sun hango mummunan kaye a zaɓe. Tabbas jama'a da dama sun kasa gane yadda al'amuran siyasar ƙasar nan ke gudana. Kana zaton a kwai wanda zai iya gudanar da mulki da aiwatar da kyawawan manufofinsa ba tare da samun nasarar jam'iyyarsa a kowane mataki ba? Kowa dai ya riga ya sani cewa mulkin ƙasa ba mutum guda ke yinsa ba, kuma kowa ya san tasirin gwamnoni da sauran kujeru a cikin mulkin ƙasa. Ko mun manta lokacin da mataimakin shugaban ƙasa a lokacin tsohon shugaban ƙasa Obasanjo wato Atiku Abubakar ya riƙa juya al'amura a zagayen farko na mulkinsu, sabo da kawai ya mallaki Gwamnoni da yawa. Ko kuna zaton jam'iyyun adawa za su so shugaban ya samu nasara a gudanar da mulki alhali su ma jam'iyyunsu suna son ƙarɓe mulkin a kowane mataki? ...

SARKIN YAKI DCP ABBA KYARI YAYI BABBAN KAMU

Image
________________________________________ Daga Abbas F. Ahmad, Kaduna. Shugaban rundinar nan ta yaki da masu aikata manyan laifuka da suka shafi fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifuka wato (IRT) DCP Abba Kyari ya kai samame a kauyen Jere dake kan hanyar Abuja-Kaduna inda ya samu nasarar kama masu fashi da makami tare da garkuwa da mutane har su 19 tare da masu sayar masu da makamai hadi da kayan sojoji. A cikin su akwai wani tsoho dan shekara 79 mai suna Abdulrashid Riba wanda ake wa lakani da Baba Wakili wanda ya Basu bindiga kirar AK47 guda 5 Kuma yana amsar kason shi a duk lokacin da akayi fashi ko akayi garkuwa da wani. Mai magana da yawun eundunar yansanda CSP Jimoh Moshood ne ya gabatar da su a gaban manema labarai a ofishin Yan sanda yanki dake garin Jere. An samu bindiga kirar AK47 guda 8 tare da wasu kirar gida, alburusai tare da Kayan sarki na sojojin Najeriya. Allah ya Kara tona asirin azzalumai ya Kuma kawo mana zaman lafiya, Amin.

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

Image
Daga S. Sadiq Gusau. An samu rarrabuwar kawuna tsakanin  magoya bayan Dan takarar da Gwamnan jihar Zamfara ya so ya gaje shi a matsayin Gwamnan Jihar Zamfara wato Mukhtar Shehu Idris da kuma masu son a kawo Rt Hon Sanusi Garba Rikiji a matsayin Dantakar Gwamna. Wasu bayanan sirri da muka samu sun nuna cewa wasu daga cikin magoya bayan Gwamna sun yi mubaya'a ga Kakakin Majalisar dokokin Jihar wato Rt Hon Sanusi Garba Rikiji. Wadannan magoya bayan suna kiran Hon Sanusi Rikiji a matsayin " RABA GARDAMA " wato a nasu hasashen Gwamnan jihar zai janye ra'ayin shi na tsayar da Mukhtar Shehu Idris wanda shine Kwamishinan Kudi na Jihar domin ganin yadda ya fuskanci turjiya daga al'umar Jihar Zamfara. A binciken da Jaridar Tauraruwa Hausa ta yi ya nuna cewa Yan Majalisar dokokin Jihar masu goyon bayan gwamnati suna tare da wannan tafiya ta shugaban su wato Rt Hon Sanusi Garba Rikiji wanda shugaban masu rinjaye a Majalisar wato Hon Isah Abdulmumini Talata Mafa...

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA NISANTA KAN SA DA HANNU WAJEN DAKATAR DA YAN MAJALISU 4

Image
Daga Aliyu B. Musa, Abuja . Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya nisantar da kan sa da sa hannu wajen dakatar da 'yan Majalisar dokokin Jihar Zamfara guda hudu da Majalisar tayi karkashin jagorancin Rt Hon Sanusi Garba Rikiji a satin da ya gabata. Wannan ya biyo bayan ganawar sirri da yayi tare da Sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma kuma Babban jigo a siyasar Zamfara wato Sanata Ahmad Sani Yarima a gidanshi dake Abuja. Gwamnan ya kuma bukaci Sanata Yarima da ya kira wadannan 'yan Majalisu domin basu hakuri  akan abunda ya faru wanda anyi shi ne ba bisa ka ka'ida ko doka ba. Rahotannin da muke samu a yau sun nuna wadannan 'yan Majalisun suna Babban Birnin tarayya wato Abuja domin ganawar sirri da shi Sanata Ahmad Sani Yarima.

SHIRE-SHIREN TSIGE MATAIMAKIN GWAMNA: YAN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA MASU GOYON BAYAN GWAMNATI SUN RARRABA MUKAMAI

Image
Daga S. Sadiq, Gusau . A shire-shiren ta na tsige mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Majalisar dokokin Jihar Zamfara ta yi rabe-raben mukamai tsakanin "Yan majalisun. Bayanan sirri da muka samu sun nuna cewa bayan sun kammala shire-shiren zasu gabatar da kuduri na tsige mataimakin gwamnan wato Malam Ibrahim Wakkala Muhammad. "Yan majalisar masu goyon bayan gwamnati sun tsara mukaman kamar haka: 1. Rt. Hon Sanusi Garba Rikiji wanda shine Kakakin Majalisar dokokin zai je a matsayin Mataimakin  Gwamna. 2. Hon. Isah Abdulmumini Talata Mafara shine shugaban masu rinjaye a Majalisar zai je a matsayin Kakakin Majalisar. 3. Hon. Aliyu Ango Kagara zai je a matsayin shugaban masu tsawatarwa. 4. Hon. Mohammadu Gummi Wanda shine mataimakin Kakakin Majalisar zai je a matsayin   shugaba Kwamitin ma'aikatar kananan hukumomi. Idan baku manta ba Majalisar dokokin karkashin jagorancin Rt Hon Sanusi Garba Rikiji ta dakatar da wasu  "Yan majalisa guda 4 masu rajin...

KUDIN GORO: NAIRA MILIYAN BAKWAI (N7,000,000.) MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA TA KARBA DAGA HANNUN CHIYAMOMA

Image
Daga S. Sadiq, Gusau. Majalisar dokokin Jihar Zamfara ta karbi Naira Miliyan Bakwai (7,000,000) a matsayin kudin goro daga kananan hukumomi Goma sha Hudu da ake dasu a Jihar. Wannan ya biyo bayan karin wa'adi da Majalisar tayi wa chiyamoman kananan hukumomi da Kansilolan su 14. Kowace karamar hukuma ta bayar da Dubu Dari Biyar inda kudin suka kama Naira Miliyan Bakwai. Shedun gani da ido ya tabbatar mana da cewa wani jami'in Majalisar dokokin ne ya karbo kudin daga hannun Kwamishinan ma'aikatar kananan hukumomi dake Jihar inda aka raba kudaden tsakanin wasu 'yan Majalisu masu goyon bayan gwamnatin. An samu yar hatsaniya wajen rabon kudin wanda wasu suka nuna rashin amincewar su ta yadda akayi wajen kasafa kudin sakamakon wasu basu samu ba.

"YAN MAJALISAR DOKOKIN DA MAJALISAR TA DAKATAR BA KAN KA'IDA BA SUN GANA DA MASU YADA LABARAI

Image
Daga S. Sadiq, Gusau. " Yan Majalisar dokokin Jihar Zamfara da aka dakata  ba bisa kan doka  ba sun yi taro da masu yada labarai yau 4/01/2019 a garin Gusau. Da yake magana a madadin "Yan Majalisar, Hon. Salisu Musa Tsafe ya karanta matsayar  su yace ba komi bane dalilin dakatar dasu a Majalisar sai saboda turjiya da suka yi na rashin amincewa  da yi ma Kundin tsarin mulkin na Kasa karan tsaye. Hon. Salisu ya kawo dalilai daga cikin Kundin tsarin mulki na cewa tsawaita lokacin Chiyamoma na jihar an yi shi ne ba bisa  ka'ida ba. Haka kuma yace doka bata bada damar kara wa duk wani zababbe lokaci ba sai dai Kantomomi. Game da dakatar dasu, Hon Salisu yace an dakatar dasu ne ba bisa doka ba saboda kafin a dakatar da su sai an kafa kwamitin bincike  da kuma sauraren korafin su. A nasu  bangaren, wanda ya gabatar da kudurin wato Hon. Isah Abdulmumini T/Mafara ya zayyano laifuka guda Uku  da yasa suka dakatar dasu. Laifukan sun hada da...

GUZURIN JUMA'AH

Image
Daga Malam Idriss Muhammad Saleh Allah ka kare mu daga hassada! من ترك الحسد استراح      Wanda ya bar hassada ya huta Allah ka cire mana Hassada Allah ka cire mana girman kai Allah ka cire mana ganin kyashi Allah ka cire mana san zuciya Allah ka yalwata Arzikin mu             Allah ka kyautata karshen mu.

SHIRIN TSIGE MATAIMAKIN GWAMNAN ZAMFARA: MAJALISAR DOKOKI TA DAKATAR DA YAN MAJALISA MASU GOYON BAYAN SA

Image
Daga S. Sadiq, Gusau. Majalisar dokokin jihar Zamfara a karkashin jogirancin Hon Rt Sanusi Garba Rikiji ta dakatar da 'Yan majalisar dokokin Jihar masu goyon bayan mataimakin Gwamnan Jihar har su Gudu (4). A zaman ta na yau Alhamis 3/1/2019 wanda Shugaban majalisar ya jagoranta, Hon. Isah Abdulmumini T/Mafara ya gabatar da kuduri na dakatar da wadannan 'Yan majalisu guda gudu (4). Yan Majalisun sun hada da Hon. Abdullahi Muhammed Dansadau wanda shine mai tsawatarwa na majalisar kuma mai wakiltar Maru ta Kudu, sai kuma Hon. Malam Mani Masaba, Hon. Mansur Ahmad Musa Bungudu Mai wakiltar Bungudu ta Yamma tare da Hon. Salisu Musa Tsafe Kainuwa Dan Majalisa  mai wakiltar Tsafe ta Gabas. Binciken da jaridar Tauraruwa tayi ya nuna cewa, dakatar da su bai rasa alaka da goyon bayan kugiyar nan ta G8 wadda tayi turjiya game da yunkurin Gwamnan jihar na dauki dora da  ya so yayi. Wata majiya da muka samu kuma tace Shugabannin majalisar suna jin tsoron idan Gwamna ya ka...

MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA TA KORI MATAIMAKAN CHIYAMOMAN KANANAN HUKUMOMI UKU

Image
Daga S. Sadiq, Gusau. Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakan Chiyamoma na Kananan  Hukumomi Uku  dake jihar. Wadannan Mataimakan sun hada da na Karamar Hukumar Zurmi, B/ Magaji da kuma Karamar Hukumar Gummi. Bayan gabatar da bukatar Gwamna na tsawaita mulkin shugabannin haka kuma nan take aka nemo a tsige wasu daga cikin mataimakan Chiyamoman. A yayin zaman majalisar, Danmajalisa mai wakiltar Maru ta Kudu a majilisar dokokin Jihar Hon. Abdullahi Mohammed Dansadau ya kalubalanci cire mataimakan Chiyamoman. Ya kara dace wa babu wani dalili da zai sa a cire su saboda babu wani laifi da sukayi wanda ya saba wa kundin tsarin mulki na kasa. Idan baku manta ba wadannan mataimakan Chiyamoman gwamnati na zargin su da kin goya mata baya inda suka dauki Yan kunguyar nan ta G8 masu adawa da dauki dora a jihar Zamfara. A labari na biyu, zamu kawo maku hirar da mukayi da wani lauya mai zaman kan shi wato Barrister Ahamad Bashir akan wannan hukuncin da Majalisar...