MAJALISAR DOKOKIN JIHAR NEJA TA GAYYACI SAKATAREN GWAMNATIN DA ALKALIN ALKALAN JIHAR
Majalisar dokokin Jihar Neja ta gayyaci Sakataren Gwamnati Ibrahim Ladan tare da Alkalin Alkalai Nasara Dan-Malam game da karin wa'adi da akayi wa shugaban Ma'aikata na Jihar.
A ranar Laraba da ta gabata ne aka gayyace su domin suyi karin bayani game da karin wa'adin mulkin da akayi wa Shugaban Ma'aikar, Alhaji Yabagi Sule duk da cewa shekarun ritayar shi daga aiki ta cika.
Shugaban ma'aikatan ya cika shekaru 60 ne a ranar 15 ga watan Janairu na wannan shekara wanda shine adadin shekarun ritaya daga aiki amma amma gwamnan ya kara mashi wa'adin mulki har zuwa 29 ga watan Mayu na wannan shekarar.
Dan Majalisa mai wakiltar Agwarra a Majalisar dokokin Jihar ne wato Ahmed Bello ne ya gabatar da kudirin a gaban Majalisar.
Dan Majalisar yace; Sashe na 208 sakin layi na (3) ya bada damar na Shugaban Ma'aikata dgaa cikin Sakataroran dindindin ko kuma wani mukami da yayi daidai da hakan.
Hon Bello ya Kara da cewa " duk maiakata dole ne subi dokokin da aka shata kan aiki" Sashi na 8 na doka ta 02807 a cikin kundin tsarin mulki na Jihar Neja ya zayyana cewa duk ma'akacin da ya kai shekara 35 yana aiki ko ya cika shekara 60 to ya cancanci ritayar dole".
Da yake karin bayani akan batun, Dan Majalisa mai wakiltar Bosso, Abdullahi Mammagi yace kara wa'adin mulkin yana iya kawo rikici a bangaren aiki a Jihar.
Hon Mammagi ya Kara da cewa 'idan har shugaban Ma'aikata ba zai yi ritaya ba lokacin da ya kamata yayi ritaya, to wasu Ma'aikatan zasu iya kin yin ritaya idan lokacin su yayi na ritaya.
Majalisar dokokin dai ta kai karshen cewa Sakataren Gwamnati tare da Alkalin Alkalai su bayyana a gaban ta ranar 29 ga watan Janairu na wannan shekara.
Kalubale gare ku 'Yan Majalisar dokokin Jihar Zamfara.
Comments
Post a Comment