"YAN MAJALISAR DOKOKIN DA MAJALISAR TA DAKATAR BA KAN KA'IDA BA SUN GANA DA MASU YADA LABARAI
Daga S. Sadiq, Gusau.
" Yan Majalisar dokokin Jihar Zamfara da aka dakata ba bisa kan doka ba sun yi taro da masu yada labarai yau 4/01/2019 a garin Gusau.
Da yake magana a madadin "Yan Majalisar, Hon. Salisu Musa Tsafe ya karanta matsayar su yace ba komi bane dalilin dakatar dasu a Majalisar sai saboda turjiya da suka yi na rashin amincewa da yi ma Kundin tsarin mulkin na Kasa karan tsaye.
Hon. Salisu ya kawo dalilai daga cikin Kundin tsarin mulki na cewa tsawaita lokacin Chiyamoma na jihar an yi shi ne ba bisa ka'ida ba. Haka kuma yace doka bata bada damar kara wa duk wani zababbe lokaci ba sai dai Kantomomi.
Game da dakatar dasu, Hon Salisu yace an dakatar dasu ne ba bisa doka ba saboda kafin a dakatar da su sai an kafa kwamitin bincike da kuma sauraren korafin su.
A nasu bangaren, wanda ya gabatar da kudurin wato Hon. Isah Abdulmumini T/Mafara ya zayyano laifuka guda Uku da yasa suka dakatar dasu. Laifukan sun hada da wasu labarai da jaridar Tauraruwa ta kawo na maganar rike masu wasu hakkokan su tare da maganar zargin cin hanci na Miliyan Dari Biyu.
Da yake karin haske kan maganar, Hon Abdullahi Muhammed Dansadau yace hukuncin da aka dauka ya nuna cewa Kakakin Majalisar wato Rt Sanusi Garba Rikiji bai san makamar aiki ba.
Comments
Post a Comment