KOTU TA BADA UMURNIN MAYARDA YAN MAJALISU 4 DA AKA DAKATAR
Daga S. Sadiq, Gusau..
Babban Kotun dake Jihar Zamfara ta umurchi Majalisar dokokin Jihar karkashin jagorancin Rt. Hon Sanusi Garba Rikiji da ta mayar da Yan Majalisu 4 da ta dakatar ba bisa kan ka'ida ba.
Yan Majalisun sun hada da:
1. Hon. Abdullahi Mohammed Dansadau
2. Hon. Malam Mani Malam Mumuni
3. Hon. Dayyabu Adamu Rijiya tare da
4. Hon. Mansur Ahmad Musa Bungudu.
Alkalin Kotun ne Justice Bello Aliyu Dan-Daba ya bada umurnin ne yau a lokacin zaman Kotun a garin Gusau babban birnin Jihar Zamfara. Alkalin ya Kara da cewa wanna oda ta zama dole haka kuma ya zama dole a basu duk wani hakki na su a matsayin su na Yan Majalisu.
Idan baku manta ba satin da ya gabata ne Majalisar dokokin Jihar Zamfara ta dakatar da wadannan Yan Majalisun ba bisa ka'ida ba inda suka kalubalanci wanna hukuncin a Kotu.
Comments
Post a Comment