SHIRIN TSIGE MATAIMAKIN GWAMNAN ZAMFARA: MAJALISAR DOKOKI TA DAKATAR DA YAN MAJALISA MASU GOYON BAYAN SA
Daga S. Sadiq, Gusau.
Majalisar dokokin jihar Zamfara a karkashin jogirancin Hon Rt Sanusi Garba Rikiji ta dakatar da 'Yan majalisar dokokin Jihar masu goyon bayan mataimakin Gwamnan Jihar har su Gudu (4).
A zaman ta na yau Alhamis 3/1/2019 wanda Shugaban majalisar ya jagoranta, Hon. Isah Abdulmumini T/Mafara ya gabatar da kuduri na dakatar da wadannan 'Yan majalisu guda gudu (4).
Yan Majalisun sun hada da Hon. Abdullahi Muhammed Dansadau wanda shine mai tsawatarwa na majalisar kuma mai wakiltar Maru ta Kudu, sai kuma Hon. Malam Mani Masaba, Hon. Mansur Ahmad Musa Bungudu Mai wakiltar Bungudu ta Yamma tare da Hon. Salisu Musa Tsafe Kainuwa Dan Majalisa mai wakiltar Tsafe ta Gabas.
Binciken da jaridar Tauraruwa tayi ya nuna cewa, dakatar da su bai rasa alaka da goyon bayan kugiyar nan ta G8 wadda tayi turjiya game da yunkurin Gwamnan jihar na dauki dora da ya so yayi.
Wata majiya da muka samu kuma tace Shugabannin majalisar suna jin tsoron idan Gwamna ya kawo kasafin kudi na shekarar bana a majalisar wadannan Yan majalisar suna iya kin aminta da shi.
Comments
Post a Comment