SHARI'A TSAKANIN UWAR JAM'IYYAR APC DA HUKUMAR ZABE MAI ZAMAN KANTA (INEC): AN SA RANAR YANKE HUKUNCI



Daga Aliyu B. Musa, Abuja.




Babbar Kotun Tarayya da ke babban Birnin Tarayya Abuja ta sa ranar  22/1/2019 a matsayin ranar da zata yanke hukunci shari'ar da take yi wadda Uwar Jam'iyyar APC ta Kasa ta sa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa akan tilasta mata da ta amshi sunayen yan takarkarun ta na Jihar Zamfara.

Idan baku manta ba Jam'iyyar APC a matakin Jihar Zamfara ta kasa gudanar da zaben fitar da gwani na Jihar har zuwa lokacin da aka rufe karbar sunayen yan takara a yayin da ita kuma uwar Jam'iyyar APC tace sun bada sunayen Yan takara ta hanyar yin sulhu. Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tace baza ta karbi sunayen  ba har sai Kotu ta bata izinin yin hakan.

Haka kuma a ranar 22/01/2019 din ne ake sa ran Jam'iyyar zata bayyana sunayen 'Yan takarar da ta bada domin su daga tutar ta a zabe mai zuwa.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA