RIKICIN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA: GWAMNA YA GANA DA YAN MAJALISU MASU GOYON BAYAN SHI
Daga S. Sadiq, Gusau.
Gwamna Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara ya gana da 'Yan Majalisu su 17 masu goyon bayan sa ranar litinin 14/1/2019 a gidan gwamnati dake fadar gwamnatin Jihar dake garin Gusau hedikwatar Babban Birnin Jihar.
A lokacin ganawar, Gwaman yayi alkawarin baiwa duk Dan Majalisar da bai samu tikitin komawa Majalisar dokokin Jihar ba wani mukami. Mukaman sun hada da Kwamishinoni, Mataimaka na Musamman wato S.A da kuma Chiyamoma na kananan hukumomi.
Da yake magana da yawun Yan Mjalisun su 17, Hon. Aminu Abubakar Danjibga ya jaddada goyon bayan su zuwa gare shi inda har yayi bayani na karyata taimakon da akace sunyi zuwa ga wata makarantar Islamiyya ta Aisha dake garin Bungudu.
Hon Danjibga ya kara da isar da sakon Sanata Ahmad Sani Yarima na cewa kada Yan Majalisu masu goyon bayan gwamnati su yadda su hada kai da sauran 'Yan Majalisu masu goyon bayan Kungiyar nan ta G8 domin suna da kudurin tsige Kakakin Majalisar wanda zai basu dama har zuwa tsige Gwamnan Jihar.
A yayin hada wannan rahoto, munyi ta kokarin ji daga bangaren Yan Majalisu 7 da suke goyon bayan Kungiyar nan ta G8 Amma mun kasa samun daya daga cikin su.
Comments
Post a Comment