SARKIN YAKI DCP ABBA KYARI YAYI BABBAN KAMU

________________________________________

Daga Abbas F. Ahmad, Kaduna.





Shugaban rundinar nan ta yaki da masu aikata manyan laifuka da suka shafi fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifuka wato (IRT) DCP Abba Kyari ya kai samame a kauyen Jere dake kan hanyar Abuja-Kaduna inda ya samu nasarar kama masu fashi da makami tare da garkuwa da mutane har su 19 tare da masu sayar masu da makamai hadi da kayan sojoji.

A cikin su akwai wani tsoho dan shekara 79 mai suna Abdulrashid Riba wanda ake wa lakani da Baba Wakili wanda ya Basu bindiga kirar AK47 guda 5 Kuma yana amsar kason shi a duk lokacin da akayi fashi ko akayi garkuwa da wani.

Mai magana da yawun eundunar yansanda CSP Jimoh Moshood ne ya gabatar da su a gaban manema labarai a ofishin Yan sanda yanki dake garin Jere. An samu bindiga kirar AK47 guda 8 tare da wasu kirar gida, alburusai tare da Kayan sarki na sojojin Najeriya.

Allah ya Kara tona asirin azzalumai ya Kuma kawo mana zaman lafiya, Amin.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA