SHIRE-SHIREN TSIGE MATAIMAKIN GWAMNA: YAN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA MASU GOYON BAYAN GWAMNATI SUN RARRABA MUKAMAI
Daga S. Sadiq, Gusau.
A shire-shiren ta na tsige mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Majalisar dokokin Jihar Zamfara ta yi rabe-raben mukamai tsakanin "Yan majalisun.
Bayanan sirri da muka samu sun nuna cewa bayan sun kammala shire-shiren zasu gabatar da kuduri na tsige mataimakin gwamnan wato Malam Ibrahim Wakkala Muhammad.
"Yan majalisar masu goyon bayan gwamnati sun tsara mukaman kamar haka:
1. Rt. Hon Sanusi Garba Rikiji wanda shine Kakakin Majalisar dokokin zai je a matsayin Mataimakin Gwamna.
2. Hon. Isah Abdulmumini Talata Mafara shine shugaban masu rinjaye a Majalisar zai je a matsayin Kakakin Majalisar.
3. Hon. Aliyu Ango Kagara zai je a matsayin shugaban masu tsawatarwa.
4. Hon. Mohammadu Gummi Wanda shine mataimakin Kakakin Majalisar zai je a matsayin shugaba Kwamitin ma'aikatar kananan hukumomi.
Idan baku manta ba Majalisar dokokin karkashin jagorancin Rt Hon Sanusi Garba Rikiji ta dakatar da wasu "Yan majalisa guda 4 masu rajin kare muradun talakawan Jihar Zamfara.
To Allah ya tarwatsa kudurinsu nayin hakan.
ReplyDelete