MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA



Daga S. Sadiq Gusau.




An samu rarrabuwar kawuna tsakanin  magoya bayan Dan takarar da Gwamnan jihar Zamfara ya so ya gaje shi a matsayin Gwamnan Jihar Zamfara wato Mukhtar Shehu Idris da kuma masu son a kawo Rt Hon Sanusi Garba Rikiji a matsayin Dantakar Gwamna.

Wasu bayanan sirri da muka samu sun nuna cewa wasu daga cikin magoya bayan Gwamna sun yi mubaya'a ga Kakakin Majalisar dokokin Jihar wato Rt Hon Sanusi Garba Rikiji.

Wadannan magoya bayan suna kiran Hon Sanusi Rikiji a matsayin "RABA GARDAMA" wato a nasu hasashen Gwamnan jihar zai janye ra'ayin shi na tsayar da Mukhtar Shehu Idris wanda shine Kwamishinan Kudi na Jihar domin ganin yadda ya fuskanci turjiya daga al'umar Jihar Zamfara.

A binciken da Jaridar Tauraruwa Hausa ta yi ya nuna cewa Yan Majalisar dokokin Jihar masu goyon bayan gwamnati suna tare da wannan tafiya ta shugaban su wato Rt Hon Sanusi Garba Rikiji wanda shugaban masu rinjaye a Majalisar wato Hon Isah Abdulmumini Talata Mafara yake jagoranci.

A wata majiya, Mashahurin Dan kasuwar Nan dake Jihar Katsina wato Alhaji Dahiru Mangal yayi wata ganawar sirri da Gwamnan jihar inda ya roki Gwamnan da ya kawo Rt Hon Sanusi Rikiji a matsayin raba gardama wanda suruki ne a wajen shi. Haka kuma ya gana da Sanatan Zamfara ta yamma wato Sanata Ahmad Sani Yarima duk akan wannan bukata tashi.

Comments

Popular posts from this blog

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA