KUDIN GORO: NAIRA MILIYAN BAKWAI (N7,000,000.) MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA TA KARBA DAGA HANNUN CHIYAMOMA
Daga S. Sadiq, Gusau.
Majalisar dokokin Jihar Zamfara ta karbi Naira Miliyan Bakwai (7,000,000) a matsayin kudin goro daga kananan hukumomi Goma sha Hudu da ake dasu a Jihar.
Wannan ya biyo bayan karin wa'adi da Majalisar tayi wa chiyamoman kananan hukumomi da Kansilolan su 14. Kowace karamar hukuma ta bayar da Dubu Dari Biyar inda kudin suka kama Naira Miliyan Bakwai.
Shedun gani da ido ya tabbatar mana da cewa wani jami'in Majalisar dokokin ne ya karbo kudin daga hannun Kwamishinan ma'aikatar kananan hukumomi dake Jihar inda aka raba kudaden tsakanin wasu 'yan Majalisu masu goyon bayan gwamnatin.
An samu yar hatsaniya wajen rabon kudin wanda wasu suka nuna rashin amincewar su ta yadda akayi wajen kasafa kudin sakamakon wasu basu samu ba.
Comments
Post a Comment