MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA TA KORI MATAIMAKAN CHIYAMOMAN KANANAN HUKUMOMI UKU
Daga S. Sadiq, Gusau.
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakan Chiyamoma na Kananan Hukumomi Uku dake jihar. Wadannan Mataimakan sun hada da na Karamar Hukumar Zurmi, B/ Magaji da kuma Karamar Hukumar Gummi.
Bayan gabatar da bukatar Gwamna na tsawaita mulkin shugabannin haka kuma nan take aka nemo a tsige wasu daga cikin mataimakan Chiyamoman.
A yayin zaman majalisar, Danmajalisa mai wakiltar Maru ta Kudu a majilisar dokokin Jihar Hon. Abdullahi Mohammed Dansadau ya kalubalanci cire mataimakan Chiyamoman. Ya kara dace wa babu wani dalili da zai sa a cire su saboda babu wani laifi da sukayi wanda ya saba wa kundin tsarin mulki na kasa.
Idan baku manta ba wadannan mataimakan Chiyamoman gwamnati na zargin su da kin goya mata baya inda suka dauki Yan kunguyar nan ta G8 masu adawa da dauki dora a jihar Zamfara.
A labari na biyu, zamu kawo maku hirar da mukayi da wani lauya mai zaman kan shi wato Barrister Ahamad Bashir akan wannan hukuncin da Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta yanke.
Allah yasa mudace
ReplyDelete