ME YASA SHUGABA BUHARI KE NEMAWA ÝAN JAM'IYYARSA AGAJIN ƘURI'UN JAMA'A?



Daga Mukhtar Jubril, Bauchi.

   



Na zo da wannan tambayar ne kuma zan amsata, bayan ganin yadda masu adawa suke neman ɗaukar hankalin jama'a tare da neman danƙarawa jama'a ƙin lafiyayyen shugaban nasu, don kawai sun hango mummunan kaye a zaɓe. Tabbas jama'a da dama sun kasa gane yadda al'amuran siyasar ƙasar nan ke gudana. Kana zaton a kwai wanda zai iya gudanar da mulki da aiwatar da kyawawan manufofinsa ba tare da samun nasarar jam'iyyarsa a kowane mataki ba?

Kowa dai ya riga ya sani cewa mulkin ƙasa ba mutum guda ke yinsa ba, kuma kowa ya san tasirin gwamnoni da sauran kujeru a cikin mulkin ƙasa. Ko mun manta lokacin da mataimakin shugaban ƙasa a lokacin tsohon shugaban ƙasa Obasanjo wato Atiku Abubakar ya riƙa juya al'amura a zagayen farko na mulkinsu, sabo da kawai ya mallaki Gwamnoni da yawa. Ko kuna zaton jam'iyyun adawa za su so shugaban ya samu nasara a gudanar da mulki alhali su ma jam'iyyunsu suna son ƙarɓe mulkin a kowane mataki? Waɗannan misalan da makamantan su shaida ne a kan cewa matuƙar shugaba na son aiwatar da gwamnatinsa cikin nasara to dole ne ya ƙarfafi nasarar jam'iyyarsa a kowane mataki. Domin ba zai taɓa zaton abu mai kyau daga ɓangaren masu adawa da shi ba.

A ƙarshe dai amsar tawa itace, dole ne sai jam'iyyar APC na da rinjayen kujeru tun daga Gwamnoni da ýan majalisu, kafin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a cikinta ya iya samun damar gudanar da mulkinsa cikin nasara. Kuma a kan wannan ne mai girma shugaban ƙasa ke tsayin daka wajen ganin jam'iyyar APC ta lashe dukkanin kujerunta a zaɓuɓɓuka masu zuwa. Har yau a kwai buƙatar mu daɗa wayar da kan mu game da yadda muke yin soyayyar siyasa da kuma adawar siyasa, in ba haka ba ba za mu taɓa samun ci gaba a irin siyasar da mukeyi yanzu ba.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA