SANARWA DAGA RUNDINAR SOJOJIN NAJERIA




Rundinar dakarun sojojin Najeriya ta bada sanarwar dakile wani hari da Kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram ta shirya kawowa a garin Baga na Jihar Borno. Mai magana da yawun rundinar ne wato Kanal Onyema Nwachuku ne ya sanar da haka a jiya Lahadi.


Kanal Nwachuku ya Kara da cewa, Yan ta'addan sun so su kai mummunan hari wanda suke dauke da miyagun makamai tare da motoci biyu dauke da bindigogin harbo jirgin sama da kuma manya-mayan abubuwa masu fashe wa domin kai harin kunar bakin wake.


An lalata mota daya dake dauke da kayan fashewa da kuma direban tare da 'yan ta'adda masu yawa. Haka kuma an kwato bindigogi da makamai masu yawa daga HANNUN 'yan ta'adda inda sojojij Najeriya suka bi su cikin daji.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA