MATSALAR SHA'ANIN TSARO A JIHAR ZAMFARA: BARDEN GALADIMA, ALHAJI BELLO IBRAHIM GUSAU YAYI TSOKACI AKAI
Daga Mohammad K Gusau Jihar Zamfara Jiha ce daga Cikin Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya Wadda a lokuttan baya mune Duk inda muka Shiga ake tambayar mu ya Zamfara ya Shariah kasancewar Jihar mu ce ta Farko Fara Kaddamarda aiki da Shariar musulunchi a hukumance a Duk fadin Afiraka ta yamma. A wancan lokacin mune mukafi kowace Jiha a Najeriya Zaman lafiya, Amma a Yau Babu abunda zamuce sai "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN" ganin irin yadda Jinin bayin Allah a Kullun yake kwarara a Cikin lungu da sako, Karkara da birane na Jihar Zamfara. INA GIZO KE SAKAR?? A Zaman mu Wadanda muka Shaida kuma suka amince da cewa Babu abun bauta sai Allah, Shi kadai ne ke bada Umurni gare mu Kuma Shine ya Kagi halitta to Haka nan Kuma Wajibin mune mu jibinta mashi dukkan lamarin mu na duniya da Kuma lahira. Mu Waiwaya baya mu gani Shin a baya Haka muke? Mun mance da fadar Allah da yace "Allah Bai musanya baiwar da yayima Mutane har sai idan sune suka musanya da...