ABDULAZIZ YARI YA SHIRYA ZANGA-ZANGAR KIN JININ ADAMS OSHOMOLE A JIHAR ZAMFARA
Daga Sani Ahmad Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya shirya yin zanga-zangar nuna kin jinin shugaban jam'iyyar APC ta kasa wato Kwamared Adams Oshomole gobe 25 ga watan Oktoba na shekarar 2019 a garin Gusau.
Wannan ya biyo bayan taron da wasu gwamnoni 8 suka yi wanda Gwamna ya jagoranta domin domin ganin an cire shugaban jam'iyyar a ranar Talatar da ta gabata a garin Abuja.
Yayin da suka kai kukan su, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna cikakken goyin bayan shi yadda shugaban jam'iyyar ke gudanar da mulkin shi ya kuma umurci gwamnonin da su koma wajen shugaban jam'iyyar domin samun maslaha akan matsalolin da suka faru a lokacin zaben fitar da gwani a jihohin su.
Rahotannin da muke samu sun nuna cewa Gwamnan ya bada umurnin da a dauko motoci tare da mutane zuwa babban birnin jihar wato Gusau domin gudanar da wannan zanga-zangar ta nuna kin jinin shugaban jam'iyyar APC na Kasa. Wannan bai rasa nasaba da rashin ba gwamnonin dama da bai yi ba na suyi yadda suke so wajen tsayar da 'yan takarkarun da suke so.
Comments
Post a Comment