DANTAKARA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA: AKWAI YIWUWAR UWAR JAM'IYYA TA BADA SUNAN MALAM IBRAHIM WAKKALA KO DAUDA LAWAL DARE.
Labarin da muke samu daga babbar hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa ya nuna cewa akwai yiwuwar ita uwar jam'iyyar ta kada ta fitar da sunan daya daga cikin yan takara guda biyu.
Yan takarar sun hada da Malam Ibrahim Wakkala wanda shine mataimakin gwamna mai ci yanzu ko kuma Ma'aikacin bankin First Bank wato Dr. Dauda Lawal Dare.
Uwar jam'iyyar ta kasa tayi haka ne domin kawo sasanci tsakanin yan takarkarun saboda a samu zaman lafiya a jihar bayan kasa gudanar da zaben fidda gwani da akayi wanda rikici ya biyo baya hadda rashin rayuka.
Comments
Post a Comment