AN RIKE MA WASU 'YAN MAJALISUN JIHAR ZAMFARA WADANDA BASU GOYON BAYAN GWAMNATI KUDIN ALAWUS
An hana wasu 'yan majalisu su gudu (4) kudin alawus na su na watan Agusta saboda ba su bin bayan gwamnati.
Rahoton da muka samu ya nuna cewa shugaban masu rinjayen majalisar dokokin jihar wato Honourable Isah Abdulmumini T/Mafara ne ya bada umurni zuwa ga akawun majalisar na a rike kudaden wadannan yan majalisun.
Wadanda aka rike ma alawus din sun hada da:
1. Hon Salisu Musa Tsafe
2.Hon. Dayyabu Adamu Rijiya
3. Hon Mansur Ahmad Bungudu da kuma
4. Hon Abdullahi Muhammad Dansadau.
Binciken da muka gudanar ya nuna cewa su dai wadannan yan Majalisa suna cikin bangaren da ke adawa da gwamnati wadanda ake kira da G8.
Mun kira lambobin wayoyin shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin amma basu shiga ba domin jin gaskiyar wannan lamari.
Comments
Post a Comment