'YAN TA'ADDAN BEROM SUNA YUNKURIN BOYE GASKIYA GAME DA BACEWAR JANAR IDRIS ALKALI

Daga Shafin Datti Assalafiy



Sakamakon mamayar garin Dura-Du da dakarun sojin Nigeria sukayi, shugabannin kabilar berom da kungiyoyinsu wadanda suka hada da:
-Berom Educational and Cultural Organization (BECO)
-Berom Youth Moulders Association (BYMA)
-Berom Women Development Association (BEWDA)
Sun hadu sun rubuta takardan koke (petition) da sa hannun wakilansu Ngwo Florence Jambol, Da Davou Davou, Choji Dalyop inda suke mika kokensu game da mamayar da sojoji sukayi musu cewa rundinar Operation Safe Haven (OPSH) karkashin kagorancin Manjo Janar Augustine Agundu tana yiwa rayuwarsu barazana

A cikin tardan koken sunce babban kwamandan rundinar Operation Save Haven Manjo Janar Augustine ya kira babban basaraken Dura-Du har zuwa ofishinsa a birnin Jos, yace masa ya bashi lokaci kankani yana umartanshi da ya fadawa mutanenshi su fito da gawar Janar Idris Alkali ko kuma su fuskanci fushin sojoji, abinda kwamandan sojin ya fadawa basaraken kenan kawai sai ya tashi ya fice daga office dinsa ba tare da ya saurari martanin basaraken ba kamar yadda sukace

Wannan matakin ne ya basu tsoro wanda yasa wakilan kabilar birom na jihar Pilato gaba daya suka taru suka rubuta takardan koke, bayan sun nesanta kansu daga alhakkin bacewar Janar Idris Alkali, sunce wai su basu da hannu cikin abinda ake zarginsu da aikata, sun fahimci wani yunkuri ne akeyi domin a shafe tarihin berom daga doron duniya da kuma a koresu daga kasarsu ta gado da suka gada kaka da kakkanni, don haka basu aminta da barazanar da sojoji suke musu ba, kuma motat Janar Idris Alkali da aka samu a cikin kududdufinsu wai makiyansu ne suka kawo motar suka jefa a ciki don a shafa musu kashin kaji

Sun rubuta takardan koke suke aika ma wadannan mutane kamar haka:
-Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
-Babban kwamandan sojoji na Operation Joint Task Force
-Babban Kwamandan sojoji na Operation Save Haven (OPHS)
- Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Pilato
- Shugaban hukumar SSS na jihar Pilato
- Babban sakataren kungiyar kare hakkin bil'adama na kasa
-Babban basaraken jihar Pilato (Gbong Gwom of Jos)
-Shugaban kula da al'adu na jihar Pilato
-Hukumomin kare hakkin bil'adama na duniya (Amnesty Internatiol / Human Right Watch)

Allah Ya kyauta!
Allah Ka kyautata makomar Janar Idris Alkali.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA