GWAMNA ABDULAZIZ YARI ABUBAKAR YA KAMMALA KOMAWA JAM'IYYAR PDP



Gwamna Abdulaziz Yari Abubakar na Jihar Zamfara ya kammala shire-shiren barin jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP mai alamar lema.

Wannan ya biyo bayan takaddamar da ta dabaibaye jam'iyyar APC na fitar da 'yan takara tun daga Gwamna, Sanatoci, 'yan majalisun tarayya da kuma na jiha.

Wani na hannun damar shi da ya bukaci a boye sunan shi yace Gwamnan yana kokawa  da rashin adalci da yace uwar jam'iyya ta kasa bata mashi.

Idan baku manta ba gwamnan ya sha yin barazana  ga jami'an zabe da uwar jam'iyyar ta turo wajen gudanar da zaben tare da shi kan shi shugaban jam'iyyar na kasa wato Kwamared Adams Oshomole.

Comments

  1. Karya ne babu wannan maganar dan allah kuringa kawo ingantattun labarai

    ReplyDelete
  2. Munji dadi dawannan labari;Allah yasa gaskiya ne kuma yatabbatar dashi,Allah yasa yakoma PDP,ai shehi yazama tamkar alade domin ayanzu zamfara bata buqatarshi kuma beda mafita ga taAddancinda yayi ko yachanja jam'iyya ko be chanjaba.

    ReplyDelete
  3. Mu jamiyyar PDPn zamfara bamuda wurinsa a jamiyyar mu sai dai ko ApGa ko NRM

    ReplyDelete
  4. Gwamnan Gwamnonin tarayyar Nigeria yana nan APC daram dam kuma shine sanata zamfara West, kogunan Gusau ne dan takarar APC a zamfara kuma zaku tabbatar da hakan.
    Kuma koda PDP zai koma muna tare dashi.
    Allah ya kare gwamnan Gwamnoni daga cutar makiya.
    Ameen.
    KAMAL GARBA BAWA RAWAYYA

    ReplyDelete
  5. Alhamdulillah! Daman Zamfarawa mundade muna jiran wannan ranar dashi da duk ire-irensa (AZZALUMAI) zasu fice daga jam'iyyar APC ta talakawan jahar Zamfara, kuma wallahi munanan daram-damn tareda maigirma Sanata Marafa APC amatsayin sabon gwamnan jaharmu mai albarka Zamfara.
    AYI MARAFA DA HUJJA 2019!

    ReplyDelete
  6. allahu akbar,allahu akbar,allahu akbar.governor a.a yari chairman govrs forum and former reps.member and senator come 2019.ya rigaya yafi qarfin apc nayional da duk wata jamiyar addawa,dashi aka assasa apczamfara kuma bai barinta har abda,sai dai yanuba kuyi kunya.mahasada ya bakin ciki...Nigeria sai atiku,zamfara sai koguna inshaallahu.

    ReplyDelete
  7. Allah sarki Dan fatan gwamna hakan bai dace dakaiba fa

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA