FADA YA BARKE TSAKANIN MASU NEMAN KUJERAR GWAMNA A JIHAR ZAMFARA DA MASU TAKARA BANGAREN GWAMNATI
A wani zama da akeyi na sasanci a wani otal mai suna City King Hotel dake garin Gusau Babban birnin jihar Zamfara, fada ya barke tsakanin yan takarar da ke da goyon bayan gwamnati da kuma yan kungiyar da ake kira da G8.
An fara fadan ne sakamakon musun da yayi zafi tsakanin Sanata Kabiru Garba Marafa, sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya da kuma Ikira Aliyu Bilbis wanda tsohon minista ne a lokacin gwamnati Obasanjo.
Daga karshe babban darakta na hukumar tsaro ta farin kaya ya shiga tsakani inda ya fitar da Sanata Marafa ya dauke shi zuwa ofishin su dake kan hanyar Lalan dake garin Gusau.
Idan baku manta ba yau ne ranar karshe da hukumar zabe ta kasa ta kayyade wajen bada sunayen yan takarar da zasu wakilci kowace jam'iyya a kakar zaben da za'a yi a shekarar 2019.
Comments
Post a Comment