MARTANI GA WANI DAN GUDUN HIJIRA (1)

Daga Bulama Adamu



Wani Dan gudun Hijira wanda ya fece daga Kauyensu a Jihar Borno tun kimanin 2011 ya samu mafuka a Jihar Katsina yana ta yayata karya da jita-jita cewa wai ba abunda ya chanja akan matsalar tsaro a Jihar Borno. Wannan martani ne gareshi saboda kar yasa wanda basu san halinda aka shiga a wancan lokacin da kuma halinda ake ciki a yanzu su dauki maganarsa abar rikewa.

Tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2015 an samu gagarumin matsalar tsaronda sai da ta kai kusan kimanin Kananan hukumomi (local governments) goma sha bakwai ne suka koma hannun yan boko haram. Alhamdulillahi cikin ikon Allah yanzu ba wani local government da yake hannunsu. Ba ma wanda suke hannunsu din ba, sai da ta kai ko ina cikin Jihar Borno ya zama abun tsoro ga mazaunin gida da kuma matafiyi saboda komai zai iya faruwa a kowane lokaci.  Mutane sun kasance a cikin tsoro a ko da yaushe walau a gida suke, a kan hanya ko kuma a wajen kasuwancinsu.  Kasuwanninmu, makarantu, Masallatai da coci coci sun zama abun gudu.  Yan Bindiga kan iya kai hari a kowannensu a kowance lokaci, su kashe mutane, su kona dukiya sannan suyi garkuwa da wanda suke so.  A cikin irin wannan yanayi ne har ta kai mutane suna tsoron zuwa kasuwanni da wuraren ibada.  An daina Sallar Jam’i a wasu masallatan sannan akwai lokacinda ko a cikin garin Maiduguri sai da aka daina Sallar Asuba, Magariba da kuma Isha a Masallatai.

Batun a tare hanya har ya zama ruwan dare dan a kullum sai an tare hanyoyi an yanka mutane.  Babbar hanyar da ta tashi daga Maiduguri zuwa Damaturu ita ma bata tsira ba dan akwai randa aka tare hanyar kusan na awanni uku kuma aka kashe mutane fiye da dari uku ta hanyar harbi da kuma yanka. 
Tashin bama-bamai suma sun zama ruwan dare walau a kan titi, kasuwanni, masallatai ko coci.  An kai hari barikin sojoji daban daban.  Garuruwa da dama sun zama kamar kushewa; ba mutane balle dabbobi.

Da abun yayi tsamari sai ya zamana hanyoyi da dama an rufe su ko kuma mutane sun kaurace musu.  A misali Maiduguri – Gamboru, Maiduguri – Damboa, Damaturu-Gujba-Biu, Maiduguri –Bama-Gwoza-Banki, Maiduguri – Monguno-Baga.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA