RIKICIN SIYASAR JIHAR ZAMFARA YAZO KARSHE: ABDULAZIZ YARI ZAI KOMA JAM'IYYAR SDP




Daga Aliyu B. Musa, Abuja.


Ga dukkan alamu rikicin siyasar Jihar Zamfara ya zo karshe bayan yanke shawarar da gwamna me ci yanzu yayi na barin jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar SDP wato Social Democratic Party mai alamar Doki.



Wannan ya biyo bayan zaman da yayi tare da  jagoran siyasar jihar Zamfara wato Sanata Ahmad Sani Yarima a garin Abuja domim samun sasanci wajen tsayar da 'yan takarkaru ta inda shi Gwamna ya ki amincewa da haka.

Gwamnan yace shi ba zai yadda da wannan tsari ba hasali ma ya kai kara a Babbar kotun tarayya dake garin Gusau yana jiran sakamakon shari'ar idan an masa adalchi zai tsaya idan ba'a yi ba zai fice daga jam'iyyar.

Rahotannin da muke samu daga jihar Zamfara sun nuna Gwamnan ya fara tura magoya bayan sa su karbi katin shedar zama 'yan jam'iyyar SDP kafin samun sakamakon shari'ar da make gudanarwa.

Idan baku manta ba wasu  shugabannin APC na kananan hukumomi guda biyu sun maka hukumar zabe da kuma jam'iyyar APC kara a kotu domin tabbatar da zaben fidda gwani da gwamnati tayi ikirarin tayi wanda  kwamitin da uwar jam'iyyar APC ta turo tace  ba'a yi zaben ba.

Comments

  1. Maganar banza,mutun yagina gida Kuma yafita gidan yakama haya,wannan Aiko ga maganar banza batakaiba.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA