LISSAFIN KILISSAFIN KIDAYAR KUDIN DA AKA SALWANTAR A GURIN ZABEN FITAR DA GWANI NA JAM'IYYAR PDP





Daga Datti Assalafiy




Akwai a kalla masu zaben fitar da gwani na jam'iyyyar PDP da ya gudana a jihar Rivers daleget mutum dubu hudu (4,000), Bukola Saraki ya baiwa kowani daleget daga cikinsu dalar amurka dubu daya ($1,000) idan aka canza zuwa kudin Nigeria zai koma naira dubu dari uku da hamsin (N350,000), don haka ya sayi delaget dalar amurka dubu hudu  ($4Million) wanda idan aka canza da kudin Nigeria ya zama naira biliyon daya da miliyoyin dari hudu (N1.4 Billion) adadin lissafin kudin da ya baiwa delaget kenan

Shi kuma Atiku Abubakar ya baiwa kowani delaget dalar amurka dubu biyar ($5,000) idan aka canza da kudin Nigeria ya koma naira miliyon daya da dubu dari bakwai da hamsin (N1,750,000) a kowani delaget, adadin kudin da ya kashe shine dalar amurka miliyon ashirin ($20,000,000) wanda idan aka canza da kudin Nigeria ya zama naira biliyon bakwai (N7 Billion) adadin kudin da ya kashe kenan

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike shi kuma ya baiwa kowani delaget dalar amurka dubu goma  ($10,000), gaba daya ya kashe dalar amurka dubu arba'in ($40,000,000) wanda idan aka lissafa da kudin Nigeria ya kashe naira biliyon goma sha hudu (N14,000,000,000).
Wannan shine kidayar kudin da suka kashe banda ma na sauran 'yan takarar

A jiya da nake bin diddigin abinda yake faruwa gurin zaben fitar da gwani na PDP, ance kasuwar 'yan canji kudi a garin Fatakwal sai da ya cika makil, wato suma masu canjin kudi kasuwarsu jiya ta bude

Allah Sarki talaka, anjima ana yaudararmu, kundai ji irin kudin da suka kashe a karon banza wadanda basu da amfani, sai kuma a dawo daga baya ana yaudararmu cewa gwamnatin Buhari ta jefamu cikin talauci, alhali ga wadanda suka jefa Kasar can a cikin talauci

Yanzu wannan makudan kudi da suka kashe kuna tsammanin halal dinsu ne? Kudin fa ya kai a ciyar da wasu jihohin Nigeria na shekara guda
Kuma misali idan sunci zaben haka zasu kyale ba zasu sace dukiyarmu su maye gurbin abinda suka kashe ba?

Akwai manyan masana tattalin arzikin kasa da suce bai kamata a samu talaka ba fa a Nigeria inda za'a juya arzikin kasar yadda ya kamata, amma Nigeria sai da tazo na daya a duniya a talauci da cin hanci da rashawa da almundahana da dukiyar Kasa da zamba cikin aminci, kuma duk a tsawon shekaru 16 da PDP tayi tana mulki aka samu wannan bakin cigaba da koma baya, zuwan shugaba Buhari ne ya toshe musu hanyar sata, kuma shugabannin duniya suka yaba mishi akan haka

Wallahi wajibi mu shiga taitayinmu talakawan Nigeria, kada ko da wasa mu sake yarda da wadannan miyagun mutane su shugabancemu, 'yan jari hujja ne masu taka talakawa su handame komai su cinye, basa tsoron Allah basu san wani abu waishi kunya ba

Yaa Allah muna rokonKa Ka haramta musu mulkin Nigeria Ka canza manasu da wadanda suka fisu gaskiya rikon amana da tsoron Allah.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA