KIRANA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA




Daga Malam Aminu Aliyu Gusau.



Mai girma ka sani cewar yadda musulunci ya yi horo ga talakkawa da su yi hakuri da shugaban da basu so har Allah Ya kawar da shi  haka ma ya yi horo da kada a dorawa mutane shugaban da basu so .

Annabi (saw) ya ce :" Mafi alkhairin shugaba shine wanda ya ke son jama'arsa suma suna sonshi , yana yi masu kyakkyawar addu'ah , suma suna yi mashi . Mafi sharrin shugaba shine wanda yake kin jama'arsa suma suna kinsa , yana yi masu mummunar addu'ah suma suna yi mashi " .

 Annabi (saw) ya ce daga cikin mutane uku abi zargi akwai Limamin da yake jagorantar mutane Sallah alhalin su basu sonshi . Wannan a Sallah kenan , balle a jagorancin al'ummah .

Mai girma Gwamna rantsuwar da ka yi cewar kwamiti ba zai shigo ba ya gudanar da zabe koda za ka mutu , da kiran da ka yi a fito a yi zanga-zanga duka ba daidai bane ga shugaba , ka yi kuskure . Ka tuna fa da 'yan tawaye suka zagaye gidan Sayyiduna Usman ya dauki matakin hana kowa ya fito domin bashi kariya , ya yarda ya mutu shi kadai ba tare da gitta rayuwar kowa a hadari ba saboda ya tsira da mulkinsa . Bai dauki kariyar mulkinsa ya kai ga hasarar rayukan musulmi ba .

Mai girma Gwamna ka sani cewar kuskure ka ke yi da kake daukar cewa wai kai ne Allah Ya dorawa damar fitarwa Zamfara da magajinka . Ka tuna cewa Annabi (saw) ya ce wajibi ne musulmi su kiyaye sharuddan da suka shatawa kansu . A nan akwai sharudda da duk aka yarda a kansu na dokokin da jam'iyyu zasu bi domin tsayar da 'yan takara . Mai girma Gwamna kai ne ka fara sabawa wadannan sharudda a lokacin da ka azawa kanka hakkin da ba naka kai kadai ba .

Mai girma Gwamna ka tuna cewar a lokacin da ka zartar da hukuncin zaben magajinka kai kadai tilonka ba tare da shawara da tuntubar masu ruwa da tsaki ba da rarrashin sauran masu bukata , ka sabawa wani ginshikin gudanar da mulki na musulunci - Allah Madaukakin Sarki Ya ce " Al'amarin musulmi shawara ce a tsakaninsu ".

Kirana a gareka Mai girma shine kada a matsayinka na shugaba ka ci gaba da zama sanadiyyar hasarar rayuka da dukiya a Jiharmu ta Zamfara . Ka dauki matakin sulhu da daidaitawa ko da kuwa ta kama ka bari a sake zabe , ko ma ka jaye dan takararka .

Allah Ya haskaka zuciyarka domin fahimtar abinda ya ke maslaha ga kanka da jama'ar Jihar Zamfara da Kasa baki daya .

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA