ZABEN FIDDA GWANI NA DAN TAKARAR GWAMNA A JIHAR ZAMFARA: GWAMNATI TA KASHE ZUNZURUTUN KUDI HAR NAIRA BILIYAN TAKWAS (8)
Gwamnatin jihar Zamfara ta kashe kudi har Naira Biliyan Takwas (8) wurin zaben fitar da gwani da ba'a ci nasarar gudanar dashi ba har zuwa lokacin da hukumar zabe ta kasa ta rufe amsar sunan dan yan takara daga jam'iyyu a fadin kasar.
Wani daya daga cikin jami'an jam'iyyar APC da ya bukaci a boye sunan sa da yafito daga karamar hukumar Gumi dake cikin Jihar ya bayyana haka a yayin hira da wakilin mu dake can jihar Zamfara.
Ya tabbatar mashi da cewa duk karamar hukumar da take jihar ta amshi kudi har miliyan Dari sau biyu yayin gudanar da zaben.
Kashi na farko shine zaben da babban baturen zaben da ka turo daga Abuja ya soke saboda magudi da aka tafka yayin zaben.
Kashi na biyu shine kudaden da aka raba lokacin zaben da aka tashi gudanarwa a jiya Lahadi wanda zaben bai yiwu ba saboda rikici da ya Barker tsakanin yan takarar da gwamnati ke Goya ma baya da kuma na kungiyar G8.
Comments
Post a Comment