BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNAN ZAMFARA (A.A.YARI)


Daga Yusuf Muhammad Kadauri



Amincin Allah ya tabbata gareka mai girma Gwamna dafatar kana cikin nutsuwa da koshin Lafiya a daidai lokacin da kake karanta wannan sako.

Bayan haka, Babban dalilin rubuta wannan sako shi ne TUNATARWA zuwa gareka akan matsayin da Allah ya Dorama na kula da dukiya da Rayuwar Al'umma a Matsayinka na jagoran Al'ummar jihar Zamfara.

Nasani cewa kai mai Ilimine, Mai Mulki kuma mai dukiya, Ni kuma ba kowa bane illa TALAKA Wanda yake karkashin mulkinka kuma ban kai ko kusa da matakin Ilimin Addini da na Zamani da Allah ya Albarkaceka dashi ba.
Amma ga dukkan Alamu ka manta da nauyin da Allah ya dorama, wanda kuma ka dauki Alkawari dakanka tareda da'fa ALQUR'ANI mai girma cewa zaka kare Al'ummar jihar Zamfara da dukiyoyinsu.

 Sai dai kash, duniya ta shaida cewa baka cika wannan Alkawari ba. Yana da Wahala a samu rana daya batareda Rayuwa ta salwantaba sakamakon addabar da Barayi suka yiwa  jihar Zamfara, ana Sace dukiyoyin mutane, ana Sace mutane domin neman kudin fansa, amma abun takaici shine ko da rana daya baka taba fitowa ta kowace irin kafa kayi Allah wadai tareda yunkurin ceto jihar Zamfara ba har sai da ka tabbatar da cewa duniya gaba daya ta san halinda jiharmu take ciki.

Munsani Allah yake kawo musiba kuma shi yake Maganinta, amma bazamu yi zaune mu rungume hannuwa ba cewa Allah zai kawo sauki batareda wani yunkuri ba na neman taimakonsa, Dalilin da Allah ya nadaka Shugaba shine ka jagoranci Al'umma tareda kula da Lafiya,Rayuwa da kuma dukikoyinsu.

Shi yasa kake da Jami'an yan Sanda da Sojoji dasauransu akarkashinka don kawaii kariyar Al'umma. Munsani ansamu sauki a kwanakin baya kuma har yanzu Jami'an tsaro suna iya Kokarinsu amma ina tabbatarma Al'amurran tsaro sun Kara tabarbarewa a jihar nan.

Ba Bukatar in cikaka da dogon surutu akan abunda ka riga ka sani amma ya Zama dole Matsayina na Dan Zamfara mai kishinta in tunatar dakai cewa: WALLAHI DUK RAYUWAR DA TA SALWANTA SAKAMAKON RASHIN TSARO A JIHAR ZAMFARA ALLAH ZAI TAMBAYEKA A RANAR ALKIYAMA!

Wace Amsa zaka ba Allah?
Kana Abuja wurin meeting (Taro) ko kana kasar waje wurin abunda ba lalle ne ya Amfani Jama'ar jihar Zamfara ba?

Jihar Zamfara ko kadan batayi yawan jihar Kaduna ba amma Husuma na tashi nan take Gwamnan jihar ya dauri damarar ganin Husumar ta Kwanta, YAKAI GWAURO YAKAI MARI had Allah yabashi ikon shawo kan Matsalar acikin AWA biyar ko makamancin haka.

Bai tsaya jiran sai Gwamnatin tarayya ta kawo masa daukiba.

Bai tsaya cewa laifin Jamar Kaduna bane.

Don Allah ko wanna Bai ishe ka Wa'azi ba mai girma Gwamna?

Kwanan nan Hanyar Mafara-Sokoto tazama kamar ' KARAR SHANU' sai dai Barayi su tare suyi abinda sunka dama  su loda mutane suyi cikin daji amma bamu Ji wani yunkuri daga gareka ba ya Mai girma Gwamna.
Yau ma ansace mutane Bakwai a DAURAN  cikinsu harda yan mata Tagwaye guda biyu wadanda suke kusa da yin Aure amma bamu Ji komai daga bakin ka ba Mai daraja Gwamna?

A karshe ina kiranka da kaji tsoron Allah ka tsaya KAI DA FATA domain ganin ka ceto jihar Zamfara daga cikin Bala'in da take ciki.

Dafatar Allah yasa wannan sakon ya isa gareka, yabaka ikon daukar shawara kuma yabaka ikon ceto jihar Zamfara kafin Karshen Wa'adin Mulkinka
 Ameen.

Kahuta Lafiya.
Yusuf Muhammad Kadauri
25-10-2018.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA