Daga S. Sadiq Gusau. An samu rarrabuwar kawuna tsakanin magoya bayan Dan takarar da Gwamnan jihar Zamfara ya so ya gaje shi a matsayin Gwamnan Jihar Zamfara wato Mukhtar Shehu Idris da kuma masu son a kawo Rt Hon Sanusi Garba Rikiji a matsayin Dantakar Gwamna. Wasu bayanan sirri da muka samu sun nuna cewa wasu daga cikin magoya bayan Gwamna sun yi mubaya'a ga Kakakin Majalisar dokokin Jihar wato Rt Hon Sanusi Garba Rikiji. Wadannan magoya bayan suna kiran Hon Sanusi Rikiji a matsayin " RABA GARDAMA " wato a nasu hasashen Gwamnan jihar zai janye ra'ayin shi na tsayar da Mukhtar Shehu Idris wanda shine Kwamishinan Kudi na Jihar domin ganin yadda ya fuskanci turjiya daga al'umar Jihar Zamfara. A binciken da Jaridar Tauraruwa Hausa ta yi ya nuna cewa Yan Majalisar dokokin Jihar masu goyon bayan gwamnati suna tare da wannan tafiya ta shugaban su wato Rt Hon Sanusi Garba Rikiji wanda shugaban masu rinjaye a Majalisar wato Hon Isah Abdulmumini Talata Mafa...
Daga Datti Assalafiy Babban shugaban cocin Living Faith Church worldwide Bishop David Oyedepo, da babban shugaban cocin Roman Catholic Diocese of Sokoto Bishop Matthew Hassan Kukah (babban aminin Jonah Jang), Sheikh Dr. Ahmad Gumi, Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, Tsohon Mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubkar Wadannan mutane da na lissafa sun hadu suka shiga tattaunawar sirri a masaukin tsohon shugaban Kasa Obasanjo dake Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) Oke-Mosan Abeokuta, kuma tattaunawar sirrin sun gabatar da ita ne a tsakar daren da ya gabata Cikin wadanda akayi tattaunar sirrin dasu akwai tsohon gwamnan jihar Ogun da tsohon gwamnan jihar Cross River Gbenga Daniel da Liyel Imoke, da kuma Sanata Ben Bruce da wasu manyan jiga jigan 'yan siyasa na jam'iyyar PDP. To jama'a ni dai zanja hankalinmu, wallahi duk tafiyar da akace an hadata da Bishop Matthew Hassan Kukah na rantse da girman Allah ba tafiyar alheri bace, muna da cikakken masaniya ...
Daga S. Sadiq, Gusau . Wani abunda ba'a saba gani ba musamman ga musulmi Arewacin Najeriya shine yima mutum sujada, wanda idan aka samu irin hakan abun yake zama abun al'ajabi a wurin al'umma. Lahadi 1 ga watan Satumba 2019 magoya bayan jam'iyyar APC suka kai ziyara tare da gaisuwar bangajiya ga tsohon Gwamnan Zamfara wato Abdulaziz Yari Abubakar bayan ya dawo daga aikin hajji. Abunda ya bada mamaki shine yin sujada tare da fashewa da kuka da wani tsohon Danmajalisa yayi mai suna Hon. Mannir Gidan Jaja, wanda ya Wakilci Zurmi ta yamma a gwamnatin da ta gabata yayi yana rokon yafiya ga gwamnan domin canza jam'iyya da yayi daga APC zuwa PDP, inda ya bayyana cewa bai yi wanka ba da ma can a baya. A bunciken da jaridar Tauraruwa tayi, ta gano cewa shi dai Hon. Mannir Gidan Jaja ya canza jam'iyya daga APC zuwa PDP a watan da ya gabata sai dai bai samu karbuwa ba ga jam'iyyar PDP dalilin sa kenan na komawa tsohuwar jam'iyyar sa.
Comments
Post a Comment