MATSALAR SHA'ANIN TSARO A JIHAR ZAMFARA: BARDEN GALADIMA, ALHAJI BELLO IBRAHIM GUSAU YAYI TSOKACI AKAI
Daga Mohammad K Gusau
Jihar Zamfara Jiha ce daga Cikin Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya Wadda a lokuttan baya mune Duk inda muka Shiga ake tambayar mu ya Zamfara ya Shariah kasancewar Jihar mu ce ta Farko Fara Kaddamarda aiki da Shariar musulunchi a hukumance a Duk fadin Afiraka ta yamma.
A wancan lokacin mune mukafi kowace Jiha a Najeriya Zaman lafiya, Amma a Yau Babu abunda zamuce sai "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN" ganin irin yadda Jinin bayin Allah a Kullun yake kwarara a Cikin lungu da sako, Karkara da birane na Jihar Zamfara.
INA GIZO KE SAKAR??
A Zaman mu Wadanda muka Shaida kuma suka amince da cewa Babu abun bauta sai Allah, Shi kadai ne ke bada Umurni gare mu Kuma Shine ya Kagi halitta to Haka nan Kuma Wajibin mune mu jibinta mashi dukkan lamarin mu na duniya da Kuma lahira.
Mu Waiwaya baya mu gani Shin a baya Haka muke?
Mun mance da fadar Allah da yace "Allah Bai musanya baiwar da yayima Mutane har sai idan sune suka musanya da kawunan su?
Shin muna Rike da tsari da dokokin Musulunchi sau da kafa ko kuwa son Zuciya ya dabaibaye mu?
Shin ba a Cikin Jihar mu bane aka Samu littafin Allah a Cikin Masai ba? Muna Ganin Allah bazai Kama mu da Wannan ba? Ko muna zato wadanda suka aikata abun kawai ne musibar zata afkama, bayan Allah Yana cewa "KUJI TSORON FITINARDA BATA SHAFUWAR WADANDA SUKAYI ZALUNCHI KAWAI DAGA CIKIN KU."
Haka Kuma Babban abun bakin Ciki Shine mun fifita harkar mu ta Siyasa fiyeda harkar mu ta addini, mun Zabi muyi Siyasar ko a mutu ko ayi Rai amma Sha'anin Kariyar addinin mu mun watsar.
MAFITA:
Mafita akan halinda Jihar mu take a Ciki shine:
1. Mu tubarma Allah akan laifukan mu da kurakuran mu.
2. Muyi riko da littafin Allah da Sunnah.
3. Mu so Yan uwan mu.
4. Mu Sadar da Zumunta.
5. Mu yafi junan mu.
6. Mu yaki Son zuciyoyin mu.
7. Mu rika tunawa da Mutuwa a kowane Hali muka samu Kan mu.
8. Mu kula da Sha'anin marayu.
9. Mu Kadaita Allah a Cikin kowane lamarin mu.
10. Mu kawarda Zalunchi kowane iri a tsakanin mu.
Da Wannan nake Rokon Allah Wanda yace ku rokeni inkarba maku daya Kawo muna dawwamammen Zaman lfy a Cikin Jihar mu ta Zamfara, ya amintar damu ya kawo muna tsaro Wanda bai yankewa, ya bamu ikon komawa ga Biyar littafin Allah da Karantarwar Sunnah.
Comments
Post a Comment