INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: MUTANEN ZAMFARA NA NEMAN ADDU'AR KU
Daga Abdul Balarabe, Gusau
Barayi Yan ta'adda da sun ka addabi karamar hukumar mulki ta Zurmi sun kafa tutoci akan babban titin zirga zirga na motoci wanda ya tashi daga Zurmi zuwa Gurbin bore ta jahar Zamfara
Bayan Sun kwashe awanni suna barin Wuta tareda Garkuwa da mutane tsakanin jiya Lahadi zuwa yau Litinin sunyi garkuwa da mutane sama da mutun talatin 30 akan hanyar su ta zuwa bidar abunda suka cida iyalansu
Bayan Wannan barayin 'yan ta'adda sunkara shigowa da wani sabon bala'i Wanda idan sukayi garkuwa da mutun ya Allah Namiji ko mace to sai sunyi kokarin bata mashi rayuwa ta hanyar yin Luwadi dashi koya amince ko kada ya amince.
Yanzu haka barayin sunsa ma sunan dajin dasuke aje mutane idan sunyi garkuwa dasu ZAMFARA SAMBISA
Muna kira Zuwa ga Shugaban kasan Nageriya Muhammadu Buhari, Zamfara muna cikin tashin hankali da tabarbarewar kasuwanci da rashin tsaro wanda har yakai yanzu barayi sun amshi Wani yanki a jahar Zamfara yau Litinin.
Muna da Ministan tsaro dan jahar Zamfara ne wanda yana da damar turoma jahar Zamfara Jami'an tsaron da Zasu magance Wannan matsalar Amma yakama bakin sa yayi shiru.
Allah muna rokon ka Allah ka kawo mana agajin gaggawa a jahar .
Comments
Post a Comment