AN GANO INDA AKA BUNNE GAWAR JANAR IDRIS ALKALI


Daga Datti Assalafiy






Dakarun sojin Nigeria sun gano inda aka bunne gawar Janar Idris Alkali a wani guri mai 'dan tazara da kududdufin da aka jefa motarshi

Dazunnan babban Kwamandan rundina ta uku General Officer Commanding (GOC) 3 Division Jos, Manjo Janar Benson Akinroluyo ya bayyana cewa kwararrun karnukan sojoji (sniffer dogs) da kwararrun jami'an tattara bayanan sirrin tsaro sune suka jagoranci gano inda aka bunne gawar Janar Idris Alkali

Janar Benson ya kara da cewa matasan yankin bayan sun hallaka Janar Idris Alkali sai suka dauke gawarshi suka kai wannan gurin suka bunne, wadanda ake zargi da hannu wajen hallakashi sun bayyana cewa an sake tone gawar Janar Idris Alkali daga wannan kabarin an kai wani waje, kuma ana cigaba da gudanar da bincike

Sojoji mun gode, aci gaba da gudanar da bincike kafin hukunci ya biyo baya.
Insha Allahu karshen ta'addancin 'yan ta'addan berom a kudancin Jos ya kusa zama tarihi

Yaa Allah Ka Jikan Janar Idris Alkali sannan  karbi shahadarshi Amin.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA