Posts

Showing posts from December, 2018

MATAKIN DA RUNINAR OPERATION LAFIYA DOLE ZATA DAUKA A GARIN BAGA JIHAR BORNO

Image
Rundinar Operation Lafiya Dole tana duba yiwuwar kwashe fararen hula a wasu yankuna na Baga zata kaisu wani kebantaccen guri don ta bada dama ga manyan jiran yakin Nigeria suyi ruwan wuta akan 'yan Boko Haram da sukazo da zummar sai sun kwace ikon garin Wannan bayanin ya fito daga bakin mataimakin mai magana da yawun rundinar Operation Lafiya Dole Kanar Onyema Nwachukwu, yace rundinar Operation Lafiya Dole zata dauki wannan matakin ne domin kada harin da jiragen yakin Nigeria zasu kaddamar a zirin Baga ya taba fararen hula Jiya Boko Haram sun saki wannan hoton a harin da sukayi a Baga wanda har ofishin 'yan sanda na garin suka fasa, sai dai rundinar sojin Nigeria ta tabbatar da cewa ita ke rike da ikon garin Kuma wannan mataki da rundinar Operation Lafiya Dole zata dauka da taimakon gwamnatin jihar Borno, amma canza matsugunin ba zai shafi fararen hula da suka fito daga Bama, Dikwa da Monguno ba saboda yankinsu babu barazana sosai, wannan matakin ya shafi garin Bag...

GWAMNATIN JIHAR ZAMFARA TA RIKE WA MATAIMAKIN GWAMNA HAKKOKIN SA

Image
Daga S. Sadiq, Gusau. Gwamnati Jihar Zamfara ta karkashin jagorancin Abdulaziz Yari Abubakar ta rike wa Mataimakin Gwamnan jihar wato Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman albashi da alawus din sa har na tsawon wata bakwai (7). Wannan ya biyo bayana turjiya da ya nuna na rashin amincewa da dauki dora da Gwamnan yaso  yayi game da wanda ya so ya gaje shi a zaben da za'a yi a shekarar 2019. A wata mai kama da wannan, Gwamnatin ta rike albashin wasu masu bada shawara ga gwamna da aka san suna da alaka ko kuma goyon bayan mataimakin Gwamnan.

GUZURIN JUMA'A

Image
Daga Malam Idriss Muhammad Salih (Albany) Duk zuciyar da take  mai yafiya, to mai ita zai rayu cikin hutu. Duk wanda ya yarda da kaddara, zai rayu cikin sa'a da,dadin rayuwa. Ya ALLAH ka yi mana gafara, Rahma, Afwah, rangwame da kuma sassauci.. Ya ALLAH kayi mana tsari da bashi, kunci, talauci, hassada da kuma bakin ciki, ka kyautata karshin mu!

KA DAWO ZAMFARA NAN DA KARSHEN SATI KO KA HADU DA FUSHI NA------ Inji Shugaba Buhari

Image
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umurci Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar da ya katse hutun da ya dauka domin ya  dawo jihar Zamfara kafin karshen mako. Wannan ya faru ne sanadiyar kashe-kashe tare da garkuwa da ake da al'ummar jihar da yaki ci yaki canye wa wanda har yayi sanadiyar barkewar tarzoma a garin Tsafe hedikwatar Karamar Hukumar Tsafe a ranar Litinin da ta gabata inda aka samu asarar dukiyoyi tare da kona  sakatariyar Karamar Hukumar. A ranar Talatar nan ne Shugaba Buhari ya kira Maimartaba Sarkin Maradun ya jajanta mashi game da asarar rayukka  da dokiyoyi da akayi a Karamar Hukumar. Ya kuma yi alkawarin kawo karshen wannan ta'addanci ga wannan yaki da jihar ma baki daya.

YAN FASHI DA KUMA SATAR MUTANE DON NEMAN KUDIN FANSA SUN KASHE A QALLA MUTANE ARBA'IN CIKIN SATI BIYU A KARAMAR HUKUMAR MULKIN TSAFE.

Image
Daga Hamisu Ibrahim Tsafe. Hare-haren 'yan fashi a cikin jihar Zamfara na karuwa duk da matakan da hukumomin Najeriya ke cewa suna dauka da nufin murkushe su. Ko a yammacin ranar Asabar sai da aka kashe akalla mutum 16 a kauyen Magamin Diddi na karamar hukumar Muradun. Shugaban karamar hukumar Tsafe, Aliyu Abubakar Tsafe ya ce tsawon kwana uku ke nan 'yan bindigar na zuwa kauyen Asaula, inda rabin mutanensa suka tsere zuwa gudun hijira. "Cikin daren Asabar sun sake komawa cikin garin Asaula, sauran mutanen da ke nan suka fatattake su, suka kashe hakimin garin, suka kona gidaje da amfanin gonan yawancin mutanen da suka gudu, in ji shi." Haka kuma, duk a wannan dare sun kuma auka wa kauyen Sakiya, inda suka kashe mutane tare da sace mutum 11 ciki har mata guda uku. Aliyu Abubakar Mc ya ce kusan kowanne dare sai sun shiga gari daya zuwa biyu, su kashe mutane, su yi garkuwa da wasu, kuma su kona dukiyoyinsu. A cewarsa: "Al'ummar wannan yanki, ...

ANYI JANA'IZAR MUTUM GOMA SHA BIYAR (15) A ZAMFARA

Image
Daga Shafin Abdul Balarabe. An gabatar da jana'iza mutum 15 da yan bindiga dadi suka kashe a garin Magamin diddi da ke Maradun a jahar Zamfara. A jiya ne Wasu 'yan bindiga suka kashe akalla mutum 15 a kauyen Magamin Diddi cikin yankin karamar Hukumar Maradun ta jihar Zamfara. Allah ya kawo mana karshen wannan bala'i na ta'addanci da muke fama dashi. Ameen.

TOSHIYAR BAKI: MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA TA NEMI NAIRA MILIYAN DARI BIYU (N200,0000,000).

Image
Daga S. Sadiq, Gusau . Majalisar dokokin jihar Zamfara ta nemi Kwamishinan Ma'aikatar Kananan Hukumomi da lamurran Masaurautu tare da Shugabannin Kananan Hukumomi su Goma sha Gudu (14) da su bata zunzurutun kudi har Naira Miliyan Dari Biyu (N200,000,000) a matsayin toshiyar baki kafin ta amince da kara tsawon wa'adin mulkin zababbun shugabannin kananan  hukumomi  tare da kansilolan su a fadin jihar. A wani bincike  da muka gudanar, mun samu labarin cewa a kwanakin da suka gabata, an yi wata ganawar sirri tsakanin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar wato Rt Hon. Sanusi Garba Rikij tare da Shugaban Masu rinjaye a majalisar wato Hon. Isah Abdulmumini T/Mafara akan karin  wa'adin mulkin inda su biyu suka amince da karin  wa'adin wanda ya saba ma dokar kundin tsarin  mulki na kasa. A rahotanni da muke samu an samu rarrabuwar kawuna tsakanin 'Yan Majalisun da suke goyon bayan gwamnatin da kuma wandada suke tare da wata kungiyar 'Yan takara da ake kira d...

TA'ADDANCIN JIHAR ZAMFARA: INA GWAMNA ABDULAZIZ YARI YA SHIGA?

Image
Daga S. Sadiq, Gusau  A duk safiyar Allah sai kaji  wani rahoto maras dadin ji daga garuruwa da kauyukan dake ilahirin jihar Zamfara. Daga a shiga wannan kauyen a kashe mutane a yi gaba da dukiyoyin su sai ayi garkuwa da mutane domin amsar makudan  kudin fasa. Duk lokacin da za'a samu ire-iren wadannan hare-hare ba zaka ji Gwamnan jihar ba wato Abdulaziz Yari Abubakar yayi magana a kai ba sai dai idan abu ya faru a tura kwamiti wanda zai kai ma iyalan wadanda abun ya shafa taimakon abinci da tufafi. Duk lokacin da wannan ibtila'i ya samu ko da ace Gwamna na cikin jihar ba za ka ji wani bayani daga bakin shi ba sai dai a ari bakin shi a ci mashi albasa kamar yadda mai taimaka mashi ta hanyar watsa labarai ya saba a koda yaushe. Cikin satin nan ne da ya gabata shugaban Karamar Hukumar Tsafe wato Alh. Ali Mc Tsafe ya bayyana ma Yan Jarida cewa cikin sati daya an kashe mutum fiye da 40 haka kuma na raunata fiye da 15 a Karamar Hukumar ta Tsafe amma har yanz...

GWAMNATIN JIHAR ZAMFARA ZATA FARA KAMA MASU AMFANI DA HANYOYIN SADA ZUMUNTA WATO SOCIAL MEDIA

Image
Daga S. Sadiq, Gusau. Gwamnatin Jihar Zamfara zata fara kama tare da hukunta masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani wato social media wadanda suke rubutu game da sukar manufofi na gwamnatin jihar. Wannan ya fito ne daga bakin Kwamishinan yada labarai na jihar wato Danjari Kwatarkwashi. A zantawar da yayi da wani gidan Talabijin mai zaman kan shi mai suna Gamji Tv a Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara, Kwamishinan yace ba zasu lamunci duk wani mai amfani da wadannan kafafe ba na suka da caccakar manufofin gwamnatin Jihar saboda haka za'a kama su tare da hukunta su. A zantawar da wakilin mu yayi da wani mai amfani da wadannan kafafen yada labarai na zamani mai suna Auwal Sani yace wannan ya saba ma dokar kasa wadda ta bada damar kowa na iya fadin ra'ayin sa akan duk wani abu da ya shafi  jiha har zuwa ga kasa baki daya.

ZA'A FITAR DA SUNAYEN YAN TAKARAR JAM'IYYAR APC A JIHAR ZAMFARA

Image
Daga Aliyu B Musa, Abuja. Jam'iyyar APC ta kasa zata fitar da sunayen 'Yan takarar ta tun daga Sanatoci, Majalisar wakilai, Gwamna da kuma 'Yan majalisun jiha a sati  mai zuwa Wannan ya faru ne bayan zama da akayi na sasancin da fahimtar juna da akayi tsakanin mambobin jam'iyyar da National Working Committee (NWC) a garin Abuja. Idan baku manta ba an samu tirka-tirka wajen zaben fidda gwani da aka so ayi wanda rikice-rikice suka hana a gabatar har zuwa lokacin da hukumar zaba ta kasa ta rufe amsar 'Yan takara.

SHIGA GABAN SHARI'A BABBAN LAIFI NE A CIKIN KUNDIN TSARIN MULKI NA NAJERIA

Image
Daga S. Bello, Gusau . A yayin da ake cigaba da shari'ar da gwamnatin jihar Zamfara ta kai karar Hukumar Zabe mai zaman kanta  ta kasa tare da uwar jam'iyyar APC ta kasa akan cewa an gudanar da zaben fidda gwani na  'Yan takara a karkashin jam'iyyar APC tun daga matakin 'Yan majalisar Dattijai, wakilai, Gwamna har zuwa ga 'Yan majalisar jiha. Wasu masu goyon bayan Gwamnati sun fara alfahari, bugun gaba da kuma saye da dinka fararen kaya da zummar cewa zasu sha biki ranar Laraba ko Alhamis mai zuwa domin kuwa alkalin zai yanke hukunci da zai masu dadi. SHARI'A SABANIN HANKALI A hirar da  jaridar Tauraruwa tayi da wani ma'aikacin Kotu da ya bukaci a sakaya sunan sa ya tabbatar mana da cewa duk wani yunkuri  da akayi ko za'a yi domin juya alkiblar shari'ar domin faranta wa wani rai ba bisa  gaskiya ba to ba zai yiwu ba. Domin ya tabbatar da Alkalin da ke wannan shari'ar mutum ne mai gaskiya wanda ba wata barazanar da zata sa ya kauc...

AKWAI YIWUWAR KORAR MA'AIKACIN HUKUMAR ZABEN DA YA BADA SHEDA A ZAMFARA DAGA AIKI.

Image
Daga Muhammad A.K, Abuja. Rahoton da jaridar Tauraruwa ta samu daga Abuja ya nuna cewa akwai yiwuwar korar ma'aikacin Hukumar zabe ta kasa wato INEC mai suna Salman Uwaisu daga aiki idan har Kotu ta tabbatar cewa ya bada sheda ne akan karya. Wannan ya biyo bayan wata sheda da ya bayar na cewa anyi zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a jihar Zamfara wanda kuma hukumar zaben ta kasa reshen jihar Zamfara ta aikawa babban ofishin su dake Abuja cewa ba'a yi zaben ba wanda shi ya haddasa tirka-tirkar da ake ciki na rashin amsar sunayen Yan takara a karkashin jam'iyyar APC a jihar. Shugaban hukumar, Farfesa Yaqub ya sha nanata cewa ba zasu lamunci duk wani bara-gurbi wanda zai shafawa hukumar tasu kashin kaji ba. Haka kuma zasu dauki mataki akan duk wani mai neman bata wa hukumar ta su suna.

DUK MAI MURNA KO JIN DADIN ANA ZUBAR DA JININ AL'UMMA BAMAI IMANI BANE- Inji Maitaimakin Gwamnan Jihar Zamfara.

Image
Daga Amir A.B, Gusau. Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Dr. Ibrahim Wakkala Muhammad Liman ya bayyana cewa duk wani mai jin dadi ko murna akan zubarda jinin da akeyi na al'umma bai da imani.  Dr. Wakkala ya bayyana haka ne ranar Asabar a wurin Gagarumin taron Maulidin da hadaddiyar Kungiyar Zawiyoyi ta Jihar Zamfara ta shirya (Rabidatul Wazaayah) Wanda ya gudana a Filin Masallacin Idi da ke garin Gusau babban Birnin Jihar Zamfara. Dr. Ibrahim Wakkala yayi yabo da godiya zuwa ga Shehunnai, Mukaddimai, Muridai, Zakirai, Sha'irai da sauran al'ummar Musulmin Jihar Zamfara akan irin addu'o'in da sukeyi domin Samun Zaman lafiya a Jihar Zamfara da Nigeria baki daya, ya kuma bukaci dasu cigaba da addu'o'in samun zaman lafiya. Daga Karshe Sarkin Malaman Gusau ya roki Allah da ya gafartama wadanda suka rasa rayukkan su a sanadiyyar hare-haren da "Yan ta'adda suka kai ya Kuma roki Allah ya isarma al'ummar Musulmi akan "Yan ta'addan da...

WASU MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA SUN YI BARAZANAR KAMA WANI DAN SOCIAL MEDIA

Image
Wasu magoya  bayan Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara sunyi barazanar sa hukumomin tsaro su kama wani dan social media mai suna Ibrahim Bello Gusau (IBG). Binciken da mukayi ya nuna cewa wani Mai suna Babangida Damba  wanda ya taba tsayawa takarar Danmajalisar wakilai mai wakiltar Gusau da Tsafe ya furta haka. Shi dai Ibrahim Bello Gusau wanda ake wa lakani da IBG sananne ne fagen tua'mmali da hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Zamfara da arewancin Najeriya baki daya.

JAM'IYYAR APC TA KASA ZATA HUKUNTA GWAMNAN ZAMFARA DA WASU GWAMNONI GUDA UKU

Image
Daga AbdulNasir Bello Jam'iyyar APC ta kasa ta sha alwashin daukar hukunci mai tsanani akan Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar, Rochas  Okorocha, Amosun da kuma Akeredoku na jihar Ondo sakamakon rashin biyayya da suke ma uwar jam'iyyar. Idan baku manta ba, a cikin watan da ya gabata ne jam'iyyar APC ta nada  wani kwamiti na tuntuba da neman sasanci wajen 'ya'yan jam'iyyar da suke tunanin ba'a yi masu daidai ba amma wadannan gwamnonin suka yi biris  da matakin. Da yake magana da kafafen yada  labarai, shugaban kwamitin ya ce shugaban Jam'iyyar APC ta Kasa Kwamared Adams Oshomole zai kafa kwamitin ladabtarwa domin duba ayukkan wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar musamman Gwamnonin da suke bada goyon  bayan wadanda suke tare dasu da su shiga wata jam'iyya. Ya kara da cewa jam'iyyar APC ta gaji da yadda wadannan gwamnonin suke mata zagon kasa wajen ganin sake samun nasarar Shugaba Buhari zango na biyu inda ta kara da c...

LABARI DA DUMI-DUMI: INEC TA HANA JAM'IYYAR DA GWAMNAN ZAMFARA YA SO YA KOMA SAUYA SUNAYEN "YAN TAKARA

Image
Daga Auwal Salisu, Abuja. Hukumar zabe ta Kasa wato Inec ta hana a sauya sunayen " Yan takarar jam'iyyar SDP  wanda taso ta canza tun daga Gwamna har zuwa ga "Yan Majalisar Jihar Zamfara. Wannan ya faru ne sakamakon lokaci da ya wuce na canza sunayen " Yan takara tun ranar  1 ga Watan  Disamba. Gwamnan Abdulaziz Yari Abubakar yayi yunkurin barin jam'iyyar APC a gobe Alhamis 6 ga watan Disamba amma sakamakon cima  bayan da aka samu na rashin bari a sauya  sunayen "Yan takarar shi zuwa wata jam'iyya abun ya faskara. Mun samu labarin yanzu haka Gwamnan ya tashi daga filin  Jirgin Sama na Nmadi Azikwe dake Abuja zuwa kasar China.

TA FARU TA KARE: GWAMNAN ZAMFARA YA KAMMALA SHIRIN BARIN APC

Image
Daga Abu Siyama, Gusau . Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya kammala shire-shiren barin jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar SDP mai alamar doki. Wannan ya biyo bayan zaman da yayi da wasu kananan jam'iyu a ranar Asabar da ta gabata a garin Abuja inda  yayi zargin jam'iyyar APC ta kasa ba zata yi mashi abunda ya so ba na kakaba Kwamishinan Kudi na Jihar Zamfara wato Mukhtar Shehu Idria a matsayin wanda zai gaje shi. Wakilin mu ya tuntubi wani magoyi bayan Gwamnan wanda ya nemi a sakaya sunan shi akan maganar barin jam'iyyar APC yace 'A yanzu ba zan iya cewa komi ba amma dai komi yana iya faruwa" Idan baku manta ba hukumar zabe ta Kasa wato Inec ta lashi takobin ba zata sa sunayen 'Yan takarar jam'iyyar APC ba a zaben gama gari da za'ayi a shekarar 2019 saboda gaza  gudanar da zaben fidda gwani  da tayi har lokacin ya wuce. Daga baya hukumar tace Kotu kawai ke da hurumin da zata sa ta sa sunayen 'Yantakarar na APC daga jih...