GWAMNATIN JIHAR ZAMFARA TA RIKE WA MATAIMAKIN GWAMNA HAKKOKIN SA
Daga S. Sadiq, Gusau.
Gwamnati Jihar Zamfara ta karkashin jagorancin Abdulaziz Yari Abubakar ta rike wa Mataimakin Gwamnan jihar wato Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman albashi da alawus din sa har na tsawon wata bakwai (7).
Wannan ya biyo bayana turjiya da ya nuna na rashin amincewa da dauki dora da Gwamnan yaso yayi game da wanda ya so ya gaje shi a zaben da za'a yi a shekarar 2019.
A wata mai kama da wannan, Gwamnatin ta rike albashin wasu masu bada shawara ga gwamna da aka san suna da alaka ko kuma goyon bayan mataimakin Gwamnan.
Comments
Post a Comment