LABARI DA DUMI-DUMI: INEC TA HANA JAM'IYYAR DA GWAMNAN ZAMFARA YA SO YA KOMA SAUYA SUNAYEN "YAN TAKARA


Daga Auwal Salisu, Abuja.


Hukumar zabe ta Kasa wato Inec ta hana a sauya sunayen " Yan takarar jam'iyyar SDP  wanda taso ta canza tun daga Gwamna har zuwa ga "Yan Majalisar Jihar Zamfara.

Wannan ya faru ne sakamakon lokaci da ya wuce na canza sunayen " Yan takara tun ranar  1 ga Watan  Disamba.

Gwamnan Abdulaziz Yari Abubakar yayi yunkurin barin jam'iyyar APC a gobe Alhamis 6 ga watan Disamba amma sakamakon cima  bayan da aka samu na rashin bari a sauya  sunayen "Yan takarar shi zuwa wata jam'iyya abun ya faskara.

Mun samu labarin yanzu haka Gwamnan ya tashi daga filin  Jirgin Sama na Nmadi Azikwe dake Abuja zuwa kasar China.


Comments

  1. Allah ya kyauta, kaikayi dai koma kan Mashekiya

    ReplyDelete
  2. Allah ya raka taki gona ya dade baibar duniya ba

    ReplyDelete
  3. Masha Allah, Allah muna godiya agareka da ka nuna ma Abdul'Aziz Kai keda iko akan kowa da komai, hmmmmmmm! Kadan Kenan sai an gama mulkin uwais uba .

    ReplyDelete
  4. Dakyau dama zalunci baya dorewa

    ReplyDelete
  5. Gud bazakagane shugaba nagariba sai ranar da ya barka sanan

    ReplyDelete
  6. Wannan tayi daidai kunnuwan ne jakkan natafe

    ReplyDelete
  7. Karya guzurin bako wannan labarin kanzon kuregene

    ReplyDelete
  8. Insha Allahu duk Maison wani musulmi yayi kunya to shizaiyinta da izinin Allah Kuma muje zuwa

    ReplyDelete
  9. Gaba dai gaba dai gwamnan Gwamnoni kowa hanyar gona yaro inbayabi ubanai yabi buhun kasa Mai nauyi yaro cika ubanka yadauka ko anki ko anso kaindaine shugaba ko gobe dakai akafara dakai za,a Kare ko makiya basusoba Mai hannun kyauta na Asma,u Zaki na Yar husaini da hadiza anbuga anbarka ayi dai mugani intusa na hura wuta zamu gani

    ReplyDelete
    Replies
    1. Ashe har yanzu Dankwairo na raye.Mudai mutumin kirki muke rokon Allah.

      Delete
  10. Komai yanada lokacinsa,kuma babu mahalukin dazai iya canza abunda mahaliccinsa yatsara.
    Allah yasa mudace.

    ReplyDelete
  11. Replies
    1. Allah sarki sheihi Allah yimaka mafiata ta Alkhairi

      Delete
  12. Yadda yassaka al'umma cikin musiba ya fara ganin sakamakonsa, kadan kenanan yafara gani

    ReplyDelete
  13. Mudai Allah yazabamuna Alkhairi dan darajar annabi Muhammad s. A. W.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA