SHIGA GABAN SHARI'A BABBAN LAIFI NE A CIKIN KUNDIN TSARIN MULKI NA NAJERIA


Daga S. Bello, Gusau.



A yayin da ake cigaba da shari'ar da gwamnatin jihar Zamfara ta kai karar Hukumar Zabe mai zaman kanta  ta kasa tare da uwar jam'iyyar APC ta kasa akan cewa an gudanar da zaben fidda gwani na  'Yan takara a karkashin jam'iyyar APC tun daga matakin 'Yan majalisar Dattijai, wakilai, Gwamna har zuwa ga 'Yan majalisar jiha.

Wasu masu goyon bayan Gwamnati sun fara alfahari, bugun gaba da kuma saye da dinka fararen kaya da zummar cewa zasu sha biki ranar Laraba ko Alhamis mai zuwa domin kuwa alkalin zai yanke hukunci da zai masu dadi.

SHARI'A SABANIN HANKALI

A hirar da  jaridar Tauraruwa tayi da wani ma'aikacin Kotu da ya bukaci a sakaya sunan sa ya tabbatar mana da cewa duk wani yunkuri  da akayi ko za'a yi domin juya alkiblar shari'ar domin faranta wa wani rai ba bisa  gaskiya ba to ba zai yiwu ba. Domin ya tabbatar da Alkalin da ke wannan shari'ar mutum ne mai gaskiya wanda ba wata barazanar da zata sa ya kauce ma hanya.

A tattaunawar da mukayi da Lauya mai zaman kan sa Barista  Rabiu A. Magaji akan shari'ar yace shiga gaban Shari'a babban laifi ne wanda kundin tsarin mulki na kasa ya tanadi hukunci akan haka. Ya kuma ba masu yin haka shawara da su daina haka domin ita sharia sabanin hankali ce.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA