TA'ADDANCIN JIHAR ZAMFARA: INA GWAMNA ABDULAZIZ YARI YA SHIGA?
Daga S. Sadiq, Gusau
A duk safiyar Allah sai kaji wani rahoto maras dadin ji daga garuruwa da kauyukan dake ilahirin jihar Zamfara. Daga a shiga wannan kauyen a kashe mutane a yi gaba da dukiyoyin su sai ayi garkuwa da mutane domin amsar makudan kudin fasa.
Duk lokacin da za'a samu ire-iren wadannan hare-hare ba zaka ji Gwamnan jihar ba wato Abdulaziz Yari Abubakar yayi magana a kai ba sai dai idan abu ya faru a tura kwamiti wanda zai kai ma iyalan wadanda abun ya shafa taimakon abinci da tufafi.
Duk lokacin da wannan ibtila'i ya samu ko da ace Gwamna na cikin jihar ba za ka ji wani bayani daga bakin shi ba sai dai a ari bakin shi a ci mashi albasa kamar yadda mai taimaka mashi ta hanyar watsa labarai ya saba a koda yaushe.
Cikin satin nan ne da ya gabata shugaban Karamar Hukumar Tsafe wato Alh. Ali Mc Tsafe ya bayyana ma Yan Jarida cewa cikin sati daya an kashe mutum fiye da 40 haka kuma na raunata fiye da 15 a Karamar Hukumar ta Tsafe amma har yanzu ba wata sanarwa ta musamman daga gwamnatin jihar.
Babban abun takaici shine duk da halin rashin tsoron da ake fama dashi a jihar, Gwamnan bai bar yawace-yawacen da yake yi ba wadanda ba sune abun farko da yasa aka zabe shi ba. Kula da rayukan jama'a da dukiyoyin su shine abu na farko ga kowace gwamnati.
Ya Allah ka kawo ma Jihar Zamfara zama lafiya tare da Najeriya baki daya, amin.
Comments
Post a Comment