MATAKIN DA RUNINAR OPERATION LAFIYA DOLE ZATA DAUKA A GARIN BAGA JIHAR BORNO




Rundinar Operation Lafiya Dole tana duba yiwuwar kwashe fararen hula a wasu yankuna na Baga zata kaisu wani kebantaccen guri don ta bada dama ga manyan jiran yakin Nigeria suyi ruwan wuta akan 'yan Boko Haram da sukazo da zummar sai sun kwace ikon garin

Wannan bayanin ya fito daga bakin mataimakin mai magana da yawun rundinar Operation Lafiya Dole Kanar Onyema Nwachukwu, yace rundinar Operation Lafiya Dole zata dauki wannan matakin ne domin kada harin da jiragen yakin Nigeria zasu kaddamar a zirin Baga ya taba fararen hula

Jiya Boko Haram sun saki wannan hoton a harin da sukayi a Baga wanda har ofishin 'yan sanda na garin suka fasa, sai dai rundinar sojin Nigeria ta tabbatar da cewa ita ke rike da ikon garin

Kuma wannan mataki da rundinar Operation Lafiya Dole zata dauka da taimakon gwamnatin jihar Borno, amma canza matsugunin ba zai shafi fararen hula da suka fito daga Bama, Dikwa da Monguno ba saboda yankinsu babu barazana sosai, wannan matakin ya shafi garin Baga ne kadai domin jiragen yakin Nigeria su samu damar kaddamar da hari akan Boko Haram ba tare da fargaban harin zai taba fararen hula ba

Kanar Onyema Nwachukwu yaci gaba da cewa rundinar Operation Lafiya Dole ta fahimci yadda wasu miyagun mutane suke kokarin yin amfani da wannan damar wajen tsorata mutanen yankin Bama, Dikwa da Monguno ta yanda zasu fice daga gidajensu su dawo sansanin 'yan gudun hijira a garin Maiduguri, don haka rundinar Operation Lafiya dole tana kira garesu da su kwantar da hankalinsu suyi watsi da abinda miyagun mutanen can suke yadawa

Yau Litinin 31-12-2018 zuwa anjima kadan shugabannin rundinar Operation LAFIYA DOLE da na 'yan sanda da sauran shugabannin hukumomin tsaro zasuyi zaman tattaunawa akan halin tsaron jihar Borno tare da mukarraban gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Kashim Shettima, rundinar sojin Nigeria tana bada tabbacin cewa jama'ar Borno su kwantar da hankalinsu domin a shirye take ta karesu..

Dukkan yunkurin da wasu gurbatattu makiya zaman lafiyar Nigeria suke kitsawa wajen da yada labaran karya game da wannan yakin, rundinar sojin Nigeria zatabi diddigi tare da daukar matakin da ya dace kamar yadda Kanar Onyema Nwachukwu ya bayyana

Muna rokon Allah Ya taimaki rundinar sojin Nigeria Ya basu nasaran shafe ruhin 'yan Boko Haram a 'kasarmu Nigeria.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA