DUK MAI MURNA KO JIN DADIN ANA ZUBAR DA JININ AL'UMMA BAMAI IMANI BANE- Inji Maitaimakin Gwamnan Jihar Zamfara.


Daga Amir A.B, Gusau.



Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Dr. Ibrahim Wakkala Muhammad Liman ya bayyana cewa duk wani mai jin dadi ko murna akan zubarda jinin da akeyi na al'umma bai da imani.

 Dr. Wakkala ya bayyana haka ne ranar Asabar a wurin Gagarumin taron Maulidin da hadaddiyar Kungiyar Zawiyoyi ta Jihar Zamfara ta shirya (Rabidatul Wazaayah) Wanda ya gudana a Filin Masallacin Idi da ke garin Gusau babban Birnin Jihar Zamfara.

Dr. Ibrahim Wakkala yayi yabo da godiya zuwa ga Shehunnai, Mukaddimai, Muridai, Zakirai, Sha'irai da sauran al'ummar Musulmin Jihar Zamfara akan irin addu'o'in da sukeyi domin Samun Zaman lafiya a Jihar Zamfara da Nigeria baki daya, ya kuma bukaci dasu cigaba da addu'o'in samun zaman lafiya.


Daga Karshe Sarkin Malaman Gusau ya roki Allah da ya gafartama wadanda suka rasa rayukkan su a sanadiyyar hare-haren da "Yan ta'adda suka kai ya Kuma roki Allah ya isarma al'ummar Musulmi akan "Yan ta'addan da duk wani mai taimaka masu ga ayukkan su na ta'addanci, ya koma roki Allah ya kawo dawwamammen Zaman lafiya a Jihar Zamfara da Najeriya Baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA