TOSHIYAR BAKI: MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA TA NEMI NAIRA MILIYAN DARI BIYU (N200,0000,000).



Daga S. Sadiq, Gusau.




Majalisar dokokin jihar Zamfara ta nemi Kwamishinan Ma'aikatar Kananan Hukumomi da lamurran Masaurautu tare da Shugabannin Kananan Hukumomi su Goma sha Gudu (14) da su bata zunzurutun kudi har Naira Miliyan Dari Biyu (N200,000,000) a matsayin toshiyar baki kafin ta amince da kara tsawon wa'adin mulkin zababbun shugabannin kananan  hukumomi  tare da kansilolan su a fadin jihar.

A wani bincike  da muka gudanar, mun samu labarin cewa a kwanakin da suka gabata, an yi wata ganawar sirri tsakanin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar wato Rt Hon. Sanusi Garba Rikij tare da Shugaban Masu rinjaye a majalisar wato Hon. Isah Abdulmumini T/Mafara akan karin  wa'adin mulkin inda su biyu suka amince da karin  wa'adin wanda ya saba ma dokar kundin tsarin  mulki na kasa.

A rahotanni da muke samu an samu rarrabuwar kawuna tsakanin 'Yan Majalisun da suke goyon bayan gwamnatin da kuma wandada suke tare da wata kungiyar 'Yan takara da ake kira da G8. Haka kuma mun samu labarin cewa ba'a sanar dasu duk wata mu'amala da ta shafi gwamnatin inda wasu har an karbe shugabancin Kwamitotan su an baiwa wasu.

A wata mai kama da wannan, Gwamnan jihar Zamfara ya fice daga Kasar nan zuwa Kasar Saudi Arabia amma a iya binciken da mu kayi ya nuna cewa bai bar ragamar mulkin jihar ga kowa ba wanda wannan ya saba ma Kundin Dokar tsarin mulki na Najeriya.

Tun a shekarun baya mutane da yawa musamman na jihar Zamfara sun zargi Majalisar dokokin jihar da rashin sanin  makamar aiki inda suka zama "Yan amshin  shata ga gwamnatin jihar.


www.Facebook.com/tauraruwahausanews

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA