AKWAI YIWUWAR KORAR MA'AIKACIN HUKUMAR ZABEN DA YA BADA SHEDA A ZAMFARA DAGA AIKI.




Daga Muhammad A.K, Abuja.




Rahoton da jaridar Tauraruwa ta samu daga Abuja ya nuna cewa akwai yiwuwar korar ma'aikacin Hukumar zabe ta kasa wato INEC mai suna Salman Uwaisu daga aiki idan har Kotu ta tabbatar cewa ya bada sheda ne akan karya.

Wannan ya biyo bayan wata sheda da ya bayar na cewa anyi zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a jihar Zamfara wanda kuma hukumar zaben ta kasa reshen jihar Zamfara ta aikawa babban ofishin su dake Abuja cewa ba'a yi zaben ba wanda shi ya haddasa tirka-tirkar da ake ciki na rashin amsar sunayen Yan takara a karkashin jam'iyyar APC a jihar.

Shugaban hukumar, Farfesa Yaqub ya sha nanata cewa ba zasu lamunci duk wani bara-gurbi wanda zai shafawa hukumar tasu kashin kaji ba. Haka kuma zasu dauki mataki akan duk wani mai neman bata wa hukumar ta su suna.

Comments

  1. Hmmmmmmm, tabdi anya kuwa ya banda shaidar kowaye yafi Iowa sanin meya faru a zamfara fa, Allah ya kyauta.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA