GWAMNATIN JIHAR ZAMFARA ZATA FARA KAMA MASU AMFANI DA HANYOYIN SADA ZUMUNTA WATO SOCIAL MEDIA
Daga S. Sadiq, Gusau.
Gwamnatin Jihar Zamfara zata fara kama tare da hukunta masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani wato social media wadanda suke rubutu game da sukar manufofi na gwamnatin jihar.
Wannan ya fito ne daga bakin Kwamishinan yada labarai na jihar wato Danjari Kwatarkwashi.
A zantawar da yayi da wani gidan Talabijin mai zaman kan shi mai suna Gamji Tv a Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara, Kwamishinan yace ba zasu lamunci duk wani mai amfani da wadannan kafafe ba na suka da caccakar manufofin gwamnatin Jihar saboda haka za'a kama su tare da hukunta su.
A zantawar da wakilin mu yayi da wani mai amfani da wadannan kafafen yada labarai na zamani mai suna Auwal Sani yace wannan ya saba ma dokar kasa wadda ta bada damar kowa na iya fadin ra'ayin sa akan duk wani abu da ya shafi jiha har zuwa ga kasa baki daya.
Comments
Post a Comment