JAM'IYYAR APC TA KASA ZATA HUKUNTA GWAMNAN ZAMFARA DA WASU GWAMNONI GUDA UKU
Daga AbdulNasir Bello
Jam'iyyar APC ta kasa ta sha alwashin daukar hukunci mai tsanani akan Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar, Rochas Okorocha, Amosun da kuma Akeredoku na jihar Ondo sakamakon rashin biyayya da suke ma uwar jam'iyyar.
Idan baku manta ba, a cikin watan da ya gabata ne jam'iyyar APC ta nada wani kwamiti na tuntuba da neman sasanci wajen 'ya'yan jam'iyyar da suke tunanin ba'a yi masu daidai ba amma wadannan gwamnonin suka yi biris da matakin.
Da yake magana da kafafen yada labarai, shugaban kwamitin ya ce shugaban Jam'iyyar APC ta Kasa Kwamared Adams Oshomole zai kafa kwamitin ladabtarwa domin duba ayukkan wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar musamman Gwamnonin da suke bada goyon bayan wadanda suke tare dasu da su shiga wata jam'iyya.
Ya kara da cewa jam'iyyar APC ta gaji da yadda wadannan gwamnonin suke mata zagon kasa wajen ganin sake samun nasarar Shugaba Buhari zango na biyu inda ta kara da cewa lokaci yayi da zata cire bara-gurbi domin samun nasara.
Wannann shine saka makon Taurin Kai
ReplyDelete