TA FARU TA KARE: GWAMNAN ZAMFARA YA KAMMALA SHIRIN BARIN APC



Daga Abu Siyama, Gusau.




Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya kammala shire-shiren barin jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar SDP mai alamar doki.

Wannan ya biyo bayan zaman da yayi da wasu kananan jam'iyu a ranar Asabar da ta gabata a garin Abuja inda  yayi zargin jam'iyyar APC ta kasa ba zata yi mashi abunda ya so ba na kakaba Kwamishinan Kudi na Jihar Zamfara wato Mukhtar Shehu Idria a matsayin wanda zai gaje shi.

Wakilin mu ya tuntubi wani magoyi bayan Gwamnan wanda ya nemi a sakaya sunan shi akan maganar barin jam'iyyar APC yace 'A yanzu ba zan iya cewa komi ba amma dai komi yana iya faruwa"

Idan baku manta ba hukumar zabe ta Kasa wato Inec ta lashi takobin ba zata sa sunayen 'Yan takarar jam'iyyar APC ba a zaben gama gari da za'ayi a shekarar 2019 saboda gaza  gudanar da zaben fidda gwani  da tayi har lokacin ya wuce. Daga baya hukumar tace Kotu kawai ke da hurumin da zata sa ta sa sunayen 'Yantakarar na APC daga jihar Zamfara.

Gwamnan ya sa ranar 6 ga watan Disamba da zai fice daga jam'iyyar APC zuwa SDP.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA