Posts

Showing posts from June, 2018

JIHAR ZAMFARA TANA BUKATAR ADALCHI DAGA GWAMNATIN TARAYYA

Image
Daga Shafin Yasir Ramadan Gwale A jiya Alhamis fadar Shugaban kasa ta sanar da cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kashe Naira biliyan goma don tallafawa iyalan wadan da suka rasa 'yan uwansu a kashe kashen da aka yi a jihar filato. Anan nake amfani da wannan dama nayi kira ga Shugaban kasa da yaji tsoron Allah, ya sani zai kasance abin tuhuma a gaban Allah kan nauyin da aka dora masa na al'ummar Najeriya. Shugaban kasa ya sani babu wani ran dan Najerya da yafi wani. An kashe mutane bila adadun a jihad Zamfara fiye da wannan da ya faru a jihad Fikato, an kashe a Birnin Gwari an kashe a Taraba an kashe a gurare da dama. Amma duk wadancan kashe kashe da suka auku musamman na Zamfara ba su da kimar da Shugaban kasa zai taimakawa iyalansu da biliyan goma? Shugaban kasa kaji tsoron Allah, babu wanda yafi wani a wajenka a matsayinka na Shugaban kasa. Bai kamata Shugaban da aka fi yi masa zaton kamanta gaskiya da adalci ya dinga nuna wqriya irin wannan ba, lallai m...

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Image
Daga Shafin Datti Assalafiy Abinda miyagun bokaye 'yan tsubbu suka rubutawa na ayoyin Allah suna baiwa mata masu neman duniya su saka a pant dinsu masiface da Allah zai iya saukar mana bala'i a cikin Kasa Yaa Allah muna rokonKa kada Ka kamamu da laifin da wawayen cikinmu suke aikatawa.

RUNDINAR SOJIN SAMA NA NIGERIA TAYI SHIRIN KAIWA AGAJI A JIHAR ZAMFARA

Image
Daga shafin Datti Assalafiy Rundinar sojin sama na Nigeria ta kaddamar da gagarumin shirin tunkarar 'yan ta'addan da suka addabi jihar Zamfara ta hanyar leken asiri ta sararin samaniyar Zamfara tare da kaiwa farmaki akan 'yan ta'adda. AVM I.S Kaita ne ya wakilci shugaban sojojin saman Nigeria AVM Sadik Abubakar wajen kaddamar da jiragen yakin da za'ayi aiki dasu a jihar ta Zamfara. Sannan daga bangaren rundinar sojojin Kasa Operation Rainin Ido sun fara aiki tare da manyan kayan yaki na zamani sun bazama jihar Zamfara kuma tuni har sun fara aiki kamar yadda aka tsara. Daga bangaren rundinar 'yan Sanda kamar yadda na fada kwanaki ana shirin tura dubban 'yan sandan kwantar da tarzoma (mopol) da kwararrrun 'yan sanda masu tunkarar ayyukan ta'addanci (counter terrorist unit) zuwa jihar Zamfara. Akwai yakinin cewa gwamnatin Baba Buhari tayi kyakkyawan shirin kawo karshen masu aikata ta'addanci a jihar Zamfara da taimakon Allah....

KWARARREN JAMI'IN DAN SANDA MAI BASIRA DCP ABBA KYARI YAYI BABBAN KAMU

Image
Daga Shafin Datti Assalafiy Akwai fadakarwa da darasi cikin wannan rubutun a daure a karanta har karshe. Kwanaki rundinar sojin Nigeria ta fitar da sanarwan bacewar daya daga cikin jami'anta mai mukamin Laftanar sunansa Laftanar Abubakar Yahya Yusuf (sojan ruwa ne) Abinda ya faru shine rundinar 'yan sanda a jihar Fatakwal sun sami rahoton mutuwar budurwan shi wannan offisan soja Laftanar Abubakar da ya bace, sunanta Lorren, ta mutu a cikin dakin offisan dake Borikiri Quarters Port-harcourt, sannan kuma aka nemi shi sojan aka rasa babu labarinsa, dalilin da yasa kenan rundinar sojin Nigeria har ta fitar da sanarwan neman jami'inta da ya bace Shine sai aka bada binciken bacewar jami'in sojan ga rundinar IGP Intelligence Response Team (IRT) wanda DCP Abba Kyari yake yiwa shugabanci, inda suka fara bincike da bin diddigi da tattara bayanan sirrin tsaro akan bacewar jami'in sojan da kuma mutuwar budurwansa a dakinsa, binciken rundinar DCP Abba Kyari ya kaisu ...

MATSALAR TSARON ZAMFARA: GWAMNA YAYI RANTSUWA

Image
A jiya ne Laraba  13/06/2018 wanda yayi dai dai da 28 ga watan Ramadan 1439 gwamna Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara yayi rantsuwa game da wanke kan shi akan sa hannu da wasu suke zargin gwamnatin shi akan matsalar tsaro. Gwaman yayi rantsuwa ne a gidan gwamnatin Jihar Zamfara in da yace "Na rantse da Allah babu wani abu da jami'an tsaro suka bukata gareni ban yi ba game da matsalar nan ta tsaro. Amma matsalar nan taki ci taki canyewa.  Sannan Idan nasan makasudin wannan bala'i ko ina da sa hannu ciki kada Allah Ya bani abunda nake nema duniya da lahira". Gwamnan ya jara da cewa " Nayi mamaki ace kwana 9 bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin turo karin jami'an tsaro a jihar Zamfara amma har yanzu shiru kake ji" Idan baku manta ba, matsalar tsaro abu ne da ya addabi mutanen karkara na Jihar Zamfara inda ko kwanan nan kauyuka fiye da 50 suka tarwatse da kuma samun  hasarar rayuka fiye da 100.

ITA DAI WANNAN RAYUWA ABAR TSORO CE KUMA BABBAN DARASI GA MASU HANKALI

Image
Daga Shafin Datti Assalafiy Tsohon gwamnan jihar Pilato Joshua Dariye kuma sanata mai ci a jam'iyyar APC kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 14 a gidan yari sakamakon sace dukiyar jihar da yayi lokacin yana mulki, saura Jonah Jang insha Allah (Yaa Allah Ka jikan musulmin jihar Pilato wadanda akayiwa kisan ta'addanci  aka gasa namansu akaci akayi video aka nunawa duniya saboda tsabagen nuna isa da samun daurin gindin gwamnoninsu) Allah dai ba azzalumin bawanSa ba. Kuma wannan hukunci da kotu ta yanke masa kamar raddi ne ga 'yan adawa wadanda suke cewa gwamnatin Baba Buhari bata tuhumar 'ya'yan jam'iyyarta na APC sai na jam'iyyar adawa, yanzu kuma ko me 'yan adawa zasuce oho? Ace mutum ya gama Gwamna, yana matsayin sanata maici, ya mallaki komai da dukiya karshe ya kare a wannan matsayi har da zubar da hawaye a idon duniya watakila a gidan yari za'a mutu, to babban abin kunya ne da tozarta gareshi Gwamnatin Baba Buhari ba sani ba sabo wan...

TSARON AL'UMMA SHINE GABA DA KOMAI

Image
Daga Hafiz Balarabe Gusau Hakika dukkan Al'ummar da basu da wada taccen tsaro Al'umma ce dake da na kasu babba" domin kuwa hankali baya kwantuwa a cikinta, zaman lafiya yayi hannun riga a cikinsu, kullum baya zasu zama maimakon cigba da habaka..................... Tashin hankali da kisan kare dangi da akeyiwa Al'umma a karkararmu, abun kullum kara ta'azzara yakeyi. Idan ka ganewa idanuwanka hanlin da jama'ar karkara suke ciki a Jihar Zamfara hanakali zai tashi matuka zakayi tunanin anya a kwai jami'in tsaro a jihar nan kuwa ko cikin kasar nan ma kuwa? Dukkan mai tausayi zai tausayawa bayin Allah mazauna karkara dake cikin jihar Zamfara mu samman a wannan karnin. Shin shugaban kasa *Muhammadu Buhari* ya san halin da Al'ummar jihar Zamfara ma suke ciki kuwa? Shin ko shugaban kasa ya san adadin rayukan da aka kashe a cin wannan watan na azumin ramadan kuwa? Sun haura sama da mutum dari a jihar Zamfara wadanda basuji ba basu ganiba? Shin kan...

ZANCEN GASKIYA DA ADALCHI

Image
Daga Shafin Datti Assalafiy Maigirma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai yace duk wanda yake kaunar Nigeria da zaman lafiya zai yabi Maigirma shugaban rundinar 'yan sandan Nigeria IGP Ibrahim K. Idris sakamakon kame 'yan ta'addan da suka kaddamar da ta'addanci a bankin Offa inda suka hallaka mutane 33 da kokarin da IGP Ibrahim K Idris yayi wajen bankada asirin masu daukar nauyin 'yan ta'addan Wannan shine zance na adalci, amma abin takaici aka samu 'yan Nigeria suke ganin cewa zargin da rundinar 'yan sandan Nigeria tayi wa sanata Bukola Saraki sharri ne duk da kwararan dalilai da shaidu da aka gabatar. Abinda nayi imani dashi shine babban mutum a siyasar Nigeria shahararren mai arziki irin Bukola saraki ace an masa sharri da kazafi kuma yana da tabbacin cewa sharri aka masa da tuntuni ya tafi kotu domin a wankeshi amma ya kasa zuwa, nasan wannan mutumin yana da dukiyar da za iya zuwa har kotun duniya domin a wankeshi daga zargi kuma ya buka...

YUNKURIN GWAMNATIN BUHARI NA KAMA OBASANJO

Image
Daga Shafin Datti Assalafiy BBC Hausa sun ruwaito labarin cewa tsohon shugaban Kasa Obasanjo ya bayyana zargin cewa shugaban Kasa Buhari yana shirin kamashi ta hanyar tattara shaidun boge... Haba Obasanjo ai indai kana da gaskiya bai kamata ba ma ka bayyanawa duniya cewa ana shirin kama ka, sai ka bari idan har an kama ka gaskiyarka ta kubutar dakai idan kana da ita Muna kara tunatar da shugaba Buhari a tuntubi Obasanjo naira biliyon ko miliyon nawa ya baiwa su Abubakar Shekau lokacin da yaje garin Maiduguri ta'aziyar mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram na farko Muhammad Yusuf Ko da yake a lokacin Abubakar Shekau sojoji sun harbeshi a kafa ya boye a wani gida cikin garin Maiduguri kafin suka sulale dashi zuwa Kano inda yayi jinyar harbin da aka masa, watakila da irin kudin da Obasanjo ya basu aka yiwa Shekau jinya kafin shigarsa jejin Sambisa karshen shekarar 2012 Allah Ka shiga tsakaninmu da miyagun mutane azzalumai 'yan kwangilar rusa arewa da sunan Boko Haram

AN FARA SHIRIN GAMAWA DA 'YAN TA'ADDAN DA SUKA ADDABI JIHAR ZAMFARA

Image
Daga Shafin Datti Assalafy Gaskiya ta'addancin da 'yan bindiga suke aikatawa a jihar Zamfara abin ya kai makura har da na rainin wayo, shiyasa rundinar sojin Nigeria ta kaddamar da wata sabuwar bataliyar sojoji wacce aka kira da OPERATION RAININ IDO domin su kalubalanci ayyukan ta'addanci a jihar Zamfara Sannan daga bangaren rundinar 'yan Sanda Maigirma IGP Ibrahim K Idris ya bada umarni an zabo kwararrun jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma Mobile Police Force (MOPOL) daga kowace shiyya na rundinar (squadrons) dake fadin kasarnan, da kuma kwararrun 'yan sanda da suke kalubalantar ayyukan ta'addanci Counter Terrorist Unit (CTU) a yanzu haka ana shirin turasu jihar Zamfara domin yaki da wannan 'yan ta'adda Don haka 'yan uwa mu tayasu da addu'ah, shugaba Buhari da mataimakansa a fannin tsaro ba zasu taba bari su gani ana kashe jama'a haka ba tare da an dauki matakin da ya dace ba, wannan shine yakinin da muke dashi. Sanna...

AN KARKATAR DA GWAMNATIN SHUGABA BUHARI

Image
Cewar Umar Sani Dansadau Talakawan da ke arewacin Najeriya sun zabi Shugaba Buhari ne domin tunanin zai kawo gyara lura da irin mulkin da yayi a baya wanda kowa yasan an dauko gyara wanda talakawa sun fara ganin amfanin shi a wancan lokacin duk da yake gwamnatin ta shi bata yi tsawo ba. Tun bayan zabe 2015 lokacin da Shugaba Buhari ya karbi ragamar mulki mutane da dama sun sa ran su na ganin an samu tsaro, saukin rayuwa da cigaban  kasa, amma saboda matsalolin da ya gada ga gwamnatin da ta gabata, abubuwan da ya tsara basu yiwu ba. Duk da haka, talakawa sun ba Shugaba Buhari uzuri amma har yanzu babu wani canji da aka samu ganin cewa farashin kaya bai sauka ba kamar yadda yake a da ba. Duk wannan ba shine abun lura ba, yadda gwamnatin ta koma tare da karkata hankalin ta ga ayukka a yankin Kudu maso Yamma wato sashen Yarbawa. Idan muka dubi kasafin kudi na shekarun da suka gabata da kuma yanzu zamu ga cewa mafi yawancin manyan ayukka an tura su zuwa Kudu. ......Muhadu ...

ANYA SHUGABA BUHARI YASAN TA'ADDANCIN DAKE FARUWA A ZAMFARA?

Image
Jahar Zamfara Jaha  ce mai zaman lafiya a shekarun baya da suka gabata amma tun shiyoyin 2012 aka fara damun tashe-tashen hankula tsakanin Fulani da Manoma. Wannan yayi sanadiyar rasa rayuka wanda akasarin su Hausawa ne. A halin da ake ciki yanzu, wannan ta'addanci kara ta'azzura yake yi domin kullum safe ta Allah sai an samu rahoton kai hari a kauyuka da dama tare da asarar rayuka masu yawa. Abun tambaya an an shine, shin Shugaba Buhari ya san halin da jahar Zamfara take ciki a kan matsalar tsaro? Halin da Jahar Zamfara take ciki a yanzu gaskiya ko Jahar Borno bata kai yawan tashin hankalin da kuma asarar rayukka da ake samu ba. Ba shakka mutanen Zamfara suna cikin yanayi na mummunan rashin tsaro da zaman fargabaa kowane lokaci. Allah ya dawo muna da dawamammen zaman lafiya a Jahar Zamfara da Najeriya baki daya.

KIMANIN MATA DUBU BIYAR (5,000) SUKA AMFANA DA KYAUTAR ATAMFOFI DAGA MATAIMAKIN GWAMNAN ZAMFARA MALAM IBRAHIM WAKKALA

Image
Kimanin mata marasa galihu Dubu Biyar (5000) suka amfana da tallafin atamfofi daga mataimakin gwamnan Zamfara Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman domin cin bukukuwan sallah. Mataimakin Gwamnan ya bayar da tallafin ne a gidan sa da ke cikin unguwar Albarkawa dake cikin Shelkwatar Jahar. Da yake bayani wajen bada wannan tallafin, shugaban wata kungiya mai suna Wakkala Media Forum Alhaji Bello Ibrahim Gusau (Alhajin APC) yace; karancin abun dake shiga hannun Mataimakin Gwamna bai taba gadar ma shi da zuciyar talaucin kasa taimakon talakka gwargwadon hali ba. Haka kuma yace bai kwaikwayo sannan baya gasa acikin ayukkan alhairi da manufar burge talakka amma ya kanyi tarayya da masu zuciya irin ta shi ta son taimakon talakka ganin ya samu sa'ida. Shima a nashi bayanin, Shugaban kula da shafin sada zumunta na na facebook na kungiyar Wakkala Media Forum wato Alhaji Ibrahim Bello Gusau (IBG) yace so da shaukin ganin talakka ya samu sa'ida yasa har uwayen mu mata bai zubar da...