RUNDINAR SOJIN SAMA NA NIGERIA TAYI SHIRIN KAIWA AGAJI A JIHAR ZAMFARA
Daga shafin Datti Assalafiy
Rundinar sojin sama na Nigeria ta kaddamar da gagarumin shirin tunkarar 'yan ta'addan da suka addabi jihar Zamfara ta hanyar leken asiri ta sararin samaniyar Zamfara tare da kaiwa farmaki akan 'yan ta'adda.
AVM I.S Kaita ne ya wakilci shugaban sojojin saman Nigeria AVM Sadik Abubakar wajen kaddamar da jiragen yakin da za'ayi aiki dasu a jihar ta Zamfara.
Sannan daga bangaren rundinar sojojin Kasa Operation Rainin Ido sun fara aiki tare da manyan kayan yaki na zamani sun bazama jihar Zamfara kuma tuni har sun fara aiki kamar yadda aka tsara.
Daga bangaren rundinar 'yan Sanda kamar yadda na fada kwanaki ana shirin tura dubban 'yan sandan kwantar da tarzoma (mopol) da kwararrrun 'yan sanda masu tunkarar ayyukan ta'addanci (counter terrorist unit) zuwa jihar Zamfara.
Akwai yakinin cewa gwamnatin Baba Buhari tayi kyakkyawan shirin kawo karshen masu aikata ta'addanci a jihar Zamfara da taimakon Allah.
Sannan dangane da zargin wasu masu ikon Zamfara da hannu cikin ta'addancin da akeyi a jihar komai zai iya faruwa, har ake cewa gwamnan jihar Zamfara ya fito yayi rantsuwa cewa bashi da hannu ciki, ni ina ganin bai kamata a zargi kowa ba matukar babu wata shaida ko dalili akan zargin, babban muhimmin abu dai a harkan magance tsaro shine sai an raba siyasa da harkan tsaro, abar jami'an tsaro suyi aikinsu kawai.
Sannan gwamnatin tarayya karkashin umarnin shugaban Kasa ya kafa kwamitin amintattu masana tsaro suyi aikin tattara bayanan sirrin tsaron jihar Zamfara, wannan zai bada dama a fahimci lamarin gaba dayansa
Yaa Allah Ka bada Nasara ga jami'an tsaron Kasarmu Ka kawo zaman lafiya a Zamfara da sauran sassan Nigeria gaba daya.
Comments
Post a Comment