KWARARREN JAMI'IN DAN SANDA MAI BASIRA DCP ABBA KYARI YAYI BABBAN KAMU
Daga Shafin Datti Assalafiy
Akwai fadakarwa da darasi cikin wannan rubutun a daure a karanta har karshe.
Kwanaki rundinar sojin Nigeria ta fitar da sanarwan bacewar daya daga cikin jami'anta mai mukamin Laftanar sunansa Laftanar Abubakar Yahya Yusuf (sojan ruwa ne)
Abinda ya faru shine rundinar 'yan sanda a jihar Fatakwal sun sami rahoton mutuwar budurwan shi wannan offisan soja Laftanar Abubakar da ya bace, sunanta Lorren, ta mutu a cikin dakin offisan dake Borikiri Quarters Port-harcourt, sannan kuma aka nemi shi sojan aka rasa babu labarinsa, dalilin da yasa kenan rundinar sojin Nigeria har ta fitar da sanarwan neman jami'inta da ya bace
Shine sai aka bada binciken bacewar jami'in sojan ga rundinar IGP Intelligence Response Team (IRT) wanda DCP Abba Kyari yake yiwa shugabanci, inda suka fara bincike da bin diddigi da tattara bayanan sirrin tsaro akan bacewar jami'in sojan da kuma mutuwar budurwansa a dakinsa, binciken rundinar DCP Abba Kyari ya kaisu ga samun nasaran kama wani matashi mai suna Taddues Jaja 'dan shekara 28.
Bayan Abba Kyari ya kama Taddues Jaja wanda ake zargi da aikata wannan mummunan aiki ya bayyana da kansa cewa shine ya hallaka budurwan Laftanar Abubakar Yahya Yusuf domin ya boye laifin da yayiwa Laftanar Abubakar, har ila yau shi wannan Jaja shine ya hallaka Laftanar Abubakar din ta hanyar shayar dashi wata kwayar guba da ake kira "Talen" wanda yayi sanadiyar mutuwarsa, sannan sai yayi anfani da wayar Laftanar Abubakar din wajen tura sako wa abokiyar budurwan sojan mai suna Joy cewa Laftanar Abubakar ne ya kashe miki kawarki Lorren akan wani sabani da ya shiga tsakaninsu...
Bayan Jaja ya kashe Lorren da laftanar Abubakar ya kuma tura sako wa abokiyar Lorren ta wayar Laftanar Abubakar, bai tsaya anan ba sai ya dauki gawar Laftanar Abubakar din a cikin motar Laftanar Abubakar ya kai cikin jeji a Ubima ya koneshi da wuta, kashin kwarangwal (Carcass) din Laftanar Abubakar ne kuke gani a wannan hoton bayan komai na jikinsa ya cinye da wuta, lokacin da Abba Kyari ya kama Jaja shine sai ya tafi dasu zuwa cikin jejin da ya kone gawar Laftanar Abubakar, inda aka tarar babu komai wuta ya cinye sai kwarangwal dinsa da ya saura
'Yan sanda sun dauko Kwarangwal din Laftanar Abubakar tare da likitocin da suka kware wajen gano yadda akayi mutum ya mutu "Pathologists" akayi gwajin kwayar halittar Laftanar Abubakar aka tabbatar da cewa shine, sai aka wuce da kashin kwarangwal din zuwa asibitin koyarwa dake birnin Port-Harcourt (UPTH) sashin ajiyar gawa
Abubuwa da aka samu a wajen wannan mugun 'dan ta'adda (Jaja) sune kamar haka:
-Motar marigayi Laftanar Abubakar wanda shi wannan 'dan ta'addan tuni har ya sayar da motar wa wani mutum a Benin City
-Handset din marigayi Laftanar Abubakar wanda ita ma har ya sayar ma wani a garin Port-Harcourt.
'Yan sanda suna cigaba da bincike kafin a gurfanar da wannan 'dan ta'adda a kotu
DARASI DA FADAKARWA:
Da farko dai shi Marigayi Laftanar Abubakar ya dauki Jaja kamar wani yaronsa amintacce da yasan sirrinsa, amma daga karshe shi yaci amanarsa ya hallaka masa budurwa ya kuma hallakashi ya kone gawarsa, koma ya tafi da motarsa da wayarsa ya sayar ma wasu, shiyasa wannan rayuwa kowa yayi taka tsantsan, dama masu karin magana suna cewa makashinka yana tare da kai..!
Kuskure ne ka sanar da mutum sirrinka gaba daya kamar yadda yake babban kuskure ne a rayuwa ka so mutum gaba daya, haka bai kamata kaki mutum gabaki daya ba, yana faruwa makiyinka a wayi gari ya dawo masoyi kamar yadda masoyi yakan koma makiyi
MASU NEMAN MATAN BANZA SUYI KARATUN-TA-NUTSU SU TUBA SU DENA DOMIN KARSHEN TARIHIN RAYUWARSU TAYI KYAU:
Shekaran da ta gabata daidai lokaci irin wannan aka hallaka wani fitaccen 'dan siyasa a wata jihar da ba zan ambata ba, anci tsohuwar gwamnati da shi sosai har kyautar mota yanayi, na sanshi sosai sani na hakika, amma washe garin ranar da zai mutu sai yayiwa iyalanshi karya cewa zasuje hidimar siyasa a wata jiha dake makwabta.
Bayan yaje ya dawo maimakon ya koma ga iyalanshi kawai sai ya wuce dakin budurwanshi wacce dalibar makarantace, ashe ta hada baki da samarinta 'yan makaranta, suka hallaka 'dan siyasar a cikin dakinta, sukaje zasu dauke motarshi domin su sayar amma motar taki buduwa saboda tana amfani da thumbprint, suka rasa yadda zasuyi da motar shine sukaje suka yanke hannun 'dan siyasar bayan sun hallakashi, sai sukayi anfani da hannunsa da suka yanke wajen bude motar sai suka dauki gawarsa sukasa a cikin motar sukaje suka bunne a kusa da wani karamin tafki, suka tafi da motar zuwa wata jiha a kudancin Kasarnan domin su sayar, to a wajen canza musu thumbprint ne asirinsu ya tonu aka kamasu bayan anga sun fito da yankakken hannun mutum
A lokacin jama'ar jihar da 'dan siyasar ya fito basu san abinda ya faru ba, sai cewa suke ai 'yan kungiyar asiri ne suka hallaka babban 'dan siyasar da ake yiwa kallon mutumin kirki a gari, amma kunga karshen tarihinsa a dakin farkarsa ya mutu taci amanarsa, su matan banza dama tun asali basu gaji amana ba, masu nemansu kuyi taka tsantsan wallahi, tarihi dai ya munana ace mutum ya mutu a dakin farka
Allah Ya sauwake.
Comments
Post a Comment