ZANCEN GASKIYA DA ADALCHI

Daga Shafin Datti Assalafiy

Maigirma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai yace duk wanda yake kaunar Nigeria da zaman lafiya zai yabi Maigirma shugaban rundinar 'yan sandan Nigeria IGP Ibrahim K. Idris sakamakon kame 'yan ta'addan da suka kaddamar da ta'addanci a bankin Offa inda suka hallaka mutane 33 da kokarin da IGP Ibrahim K Idris yayi wajen bankada asirin masu daukar nauyin 'yan ta'addan

Wannan shine zance na adalci, amma abin takaici aka samu 'yan Nigeria suke ganin cewa zargin da rundinar 'yan sandan Nigeria tayi wa sanata Bukola Saraki sharri ne duk da kwararan dalilai da shaidu da aka gabatar.

Abinda nayi imani dashi shine babban mutum a siyasar Nigeria shahararren mai arziki irin Bukola saraki ace an masa sharri da kazafi kuma yana da tabbacin cewa sharri aka masa da tuntuni ya tafi kotu domin a wankeshi amma ya kasa zuwa, nasan wannan mutumin yana da dukiyar da za iya zuwa har kotun duniya domin a wankeshi daga zargi kuma ya bukaci a biyashi diyyan batanci amma ya kasa zuwa koda kotun magistrate a Nigeria..

Jama'ar Nigeria ya kamata muyiwa kanmu adalci sannan mu yiwa jami'an tsaron Kasarmu adalci, kullun muna korafin cewa matsalar tsaro ya tabarbare a cikin kasa jami'an tsaro sun kasa shawo kan matsalar, to ya kamata mu san da cewa babu yadda za'ayi a magance matsalar masu aikata manyan laifuka  ba tare da an dakile wadanda suke daukar nauyinsu ba, domin shi 'dan ta'adda sai ya samu bindiga kafin ya iya zuwa yayi ta'addanci

Don haka kamata yayi mu bada goyon baya ga jami'an tsaron Kasarmu su tuhumi duk wanda ake zargi da laifin tallafawa 'yan ta'adda, bai kamata a dinga goyon bayan wadanda ake zargin ba, yin haka yana matukar sanyaya gwiwar masu aikin tsaro, imba haka ba za'a tabbata cikin fuskantar barazana na 'yan bindiga da 'yan ta'adda

Muna rokon Allah Ya taimaki hukumomin tsaronmu Ya kawo mana mafita na alheri da zaman lafiya a Nigeria.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA