MATSALAR TSARON ZAMFARA: GWAMNA YAYI RANTSUWA



A jiya ne Laraba  13/06/2018 wanda yayi dai dai da 28 ga watan Ramadan 1439 gwamna Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara yayi rantsuwa game da wanke kan shi akan sa hannu da wasu suke zargin gwamnatin shi akan matsalar tsaro.

Gwaman yayi rantsuwa ne a gidan gwamnatin Jihar Zamfara in da yace "Na rantse da Allah babu wani abu da jami'an tsaro suka bukata gareni ban yi ba game da matsalar nan ta tsaro. Amma matsalar nan taki ci taki canyewa.  Sannan Idan nasan makasudin wannan bala'i ko ina da sa hannu ciki kada Allah Ya bani abunda nake nema duniya da lahira".

Gwamnan ya jara da cewa " Nayi mamaki ace kwana 9 bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin turo karin jami'an tsaro a jihar Zamfara amma har yanzu shiru kake ji"

Idan baku manta ba, matsalar tsaro abu ne da ya addabi mutanen karkara na Jihar Zamfara inda ko kwanan nan kauyuka fiye da 50 suka tarwatse da kuma samun  hasarar rayuka fiye da 100.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA