AN FARA SHIRIN GAMAWA DA 'YAN TA'ADDAN DA SUKA ADDABI JIHAR ZAMFARA

Daga Shafin Datti Assalafy




Gaskiya ta'addancin da 'yan bindiga suke aikatawa a jihar Zamfara abin ya kai makura har da na rainin wayo, shiyasa rundinar sojin Nigeria ta kaddamar da wata sabuwar bataliyar sojoji wacce aka kira da OPERATION RAININ IDO domin su kalubalanci ayyukan ta'addanci a jihar Zamfara

Sannan daga bangaren rundinar 'yan Sanda Maigirma IGP Ibrahim K Idris ya bada umarni an zabo kwararrun jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma Mobile Police Force (MOPOL) daga kowace shiyya na rundinar (squadrons) dake fadin kasarnan, da kuma kwararrun 'yan sanda da suke kalubalantar ayyukan ta'addanci Counter Terrorist Unit (CTU) a yanzu haka ana shirin turasu jihar Zamfara domin yaki da wannan 'yan ta'adda

Don haka 'yan uwa mu tayasu da addu'ah, shugaba Buhari da mataimakansa a fannin tsaro ba zasu taba bari su gani ana kashe jama'a haka ba tare da an dauki matakin da ya dace ba, wannan shine yakinin da muke dashi.

Sannan a duk lokacin da ake batun tsaro kowa yana da irin gudunmawar da zai bayar domin a inganta tsaro a cikin Kasa koda kuwa gudunmawar addu'ah ce

Muna rokon Allah Ya kawo karshen ayyukan ta'addanci a jihar Zamfara da Nigeria gaba daya.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA