AN KARKATAR DA GWAMNATIN SHUGABA BUHARI
Cewar Umar Sani Dansadau
Talakawan da ke arewacin Najeriya sun zabi Shugaba Buhari ne domin tunanin zai kawo gyara lura da irin mulkin da yayi a baya wanda kowa yasan an dauko gyara wanda talakawa sun fara ganin amfanin shi a wancan lokacin duk da yake gwamnatin ta shi bata yi tsawo ba.
Tun bayan zabe 2015 lokacin da Shugaba Buhari ya karbi ragamar mulki mutane da dama sun sa ran su na ganin an samu tsaro, saukin rayuwa da cigaban kasa, amma saboda matsalolin da ya gada ga gwamnatin da ta gabata, abubuwan da ya tsara basu yiwu ba.
Duk da haka, talakawa sun ba Shugaba Buhari uzuri amma har yanzu babu wani canji da aka samu ganin cewa farashin kaya bai sauka ba kamar yadda yake a da ba.
Duk wannan ba shine abun lura ba, yadda gwamnatin ta koma tare da karkata hankalin ta ga ayukka a yankin Kudu maso Yamma wato sashen Yarbawa. Idan muka dubi kasafin kudi na shekarun da suka gabata da kuma yanzu zamu ga cewa mafi yawancin manyan ayukka an tura su zuwa Kudu.
......Muhadu a kashi na biyu.
Comments
Post a Comment